Ido zai raina fata bayan bincike ya tono wasu badakalolin biliyoyin kudi a Majalisa

Ido zai raina fata bayan bincike ya tono wasu badakalolin biliyoyin kudi a Majalisa

  • Babban mai binciken kudi a gwamnatin tarayya, Mista Aghughu Adolphus, ya yi wata babbar fallasa
  • Aghughu Adolphus ya gano yadda aka ce an kashe N8.5bn a majalisar tarayya ba tare da ka’ida ba
  • Wannan badakala da ake zargin an tafka a baya ta shiga majalisar wakilai da majalisar dattawa

Abuja - Daily Trust tace binciken da aka gabatarwa Akawun majalisar tarayya a watan Agustan bana, ya nuna yadda aka batar da biliyoyi ba tare da bin ka’idoji ba.

Binciken ya nuna majalisar tarayya ta ki maidawa gwamnatin tarayya bashin da ta karba. Badakalar da aka bankado a binciken ya haura Naira biliyan uku.

An gano cewa an cire N219.6m da N123.3m daga albashin Sanatoci da sunan kudin motoci da gida da aka ba su bashi. Kudin nan ba su koma cikin asusun tarayya ba.

Kara karanta wannan

Bincike: Yadda ‘yan majalisun Najeriya suka karkatar da sama da Naira biliyan 5.2 a 2019

Sannan a tsakanin wannan lokaci, an zaftarewa ma’aikatan majalisa N176m da sunan harajin PAYE daga albashinsu, baya ga harajin VAT da WHT na N215.9m.

Wannan rahoto har ila yau yace a 2019, majalisa tayi ikirarin ta kashe N1.7bn wajen sayen motoci da kayan ofis. Har yau ba a ga inda aka kai wadannan kayan ba.

Majalisa
Zauren Majalisar Dattawa Hoto: Tope Brown / @NgrSenate
Asali: Facebook

Akwai wasu N423m da aka cire da nufin za a sayo motocin aiki da zanen tambarin majalisa. Binciken na Adolphus yace su ma wadannan kayan sun yi kafa.

Akwai kwangilar N276.7m da aka bada a majalisa, a nan ma ba a cire harajin kudin hatimin banki ba. Sannan an biya ma’aikata N31.9m ba tare da ka’ida ba.

Babu wanda ya sha a wannan binciken

Sahara Reporters tace bincike da Aghughu Adolphus ya yi, ya fallasa majalisar wakilan tarayya, majalisar dattawa da hukumar da ke kula da aikin majalisa ta kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari za ta karbo sabon bashi daga bankin muslunci saboda wasu dalilai

Da aka tuntubi majalisar tarayya, tace duk an shawo kan abubuwan da ke cikin rahoto Aghughu Adolphus.

Majalisa ta yi bincike, ta manta da kanta

A baya an ji kwamitin sa ido a asusun gwamnati na majalisa ya fi shekara daya ya na binciken kudin da sauran ma’aikatun tarayya suka kashe daga 2015-2018.

Shugaban kwamitin, Sanata Matthew Urhoghide yace la’akari da binciken Adolphus, an gano wasu ma’aikatu da ake zargin an sace sama da Naira biliyan 80.

Sai dai ‘yan majalisar sun manta da kansu a lokacin da suke binciken sauran masu sabawa doka. Ana zargin ‘yan majalisar da kin biyan harajin VAT da na WHT.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng