Shugabannin Ma’aikata sun yi wa asusu kar-kaf, sun wawuri N84bn inji Majalisar Dattawa

Shugabannin Ma’aikata sun yi wa asusu kar-kaf, sun wawuri N84bn inji Majalisar Dattawa

  • Majalisa ta na zargin Ma’aikatar NSITF da karkatar da dukiyar Gwamnati
  • Kwamitin Matthew Urhoghide ya ce NSITF ta barnatar da Naira biliyan 84
  • Shugaban NSITF ya musanya zargin, ya ce sam ba su karya wata doka ba

Kwamitin majalisar dattawa da ke bibiyar kudin al’umma ya dogara da rahoton mai binciken kudin gwamnati, ya na yin na sa bincike na musamman.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoton cewa Sanata Matthew Urhoghide, wanda shi ne shugaban wannan kwamiti, ya na zargin NSITF da tafka badakala.

Sanatan da ke wakiltar mazabar Edo ta kudu a majalisar dattawan ya shaida wa ‘yan jarida cewa shugabannin NSITF sun yi ta’asa ne tsakanin 2012 da 2017.

KU KARANTA: Gwamnati ta na kashe Biliyoyi kullum a bar fetur a N162

Punch ta ce Majalisar dattawa ta dauko maganar wannan bincike a ranar Litinin 28 ga watan Yuni, 2021, ta ce an wawari Naira biliyan 84 cikin shekara hudu.

Kwamitin bincike a karkashin Matthew Urhoghide

Sanata Matthew Urhoghide ya ce takardun 12 daga cikin 50 da aka gabatar a gaban kwamitinsa ya tabbatar da wannan zargin da su ke da shi a kan ma’aikatar.

Matthew Urhoghide ya koka:

“Sun sace dukiyarmu, wasu ‘yan tsirarun ma’aikata da ba su da tausayi.”
“Duk ba su da gaskiya, an same su da kashi a jikinsu. Wannan ma’aikata ta fi kowane saba doka.”

KU KARANTA: An sa ranar da za ayi ta, ta kare tsakanin Patience Jonathan da EFCC

'Yan Majalisar Dattawa
Sanata Matthew Urhoghide a Majalisa Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Zargin da ke kan wuyan NSITF

Mai binciken gwamnatin tarayya ya na zargin ma’aikatar ta NSITF da amfani da tsarin biyan albashin da hukumar yanke albashi na kasa ba ta san da shi ba.

A dalilin haka, aka kashe N38, 219, 919, 530.32 da sunan kudin ma’aikata daga 2012 zuwa 2017. Amfani da haramtaccen tsarin ya jawo asara da dukiyar al'umma.

Sai dai babban darektan hukumar ta NSITF, Dr Michael Akabogu, ya ce an amince da kudin da su ka kashe a wata wasika da aka fitar a rabar 5 ga watan Yulin 2019.

A makon nan aka ji cewa wasu ‘facaka’ da kudi da aka yi a hukumar NPA a karkashin shugabancin Hadiza Bala-Usmansun kara tashi bayan shekaru uku.

NPA ta ki biyan harajin Naira biliyan 44 sannan ta yi bindiga da wasu makudan kudin da adadinsu ya kai Naira biliyan 80 wajen bada kwangiloli da raba gidaje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel