Hotuna da bidiyon matashiyar basarakiya da ta karya tarihin shekara100 na kabilar Urhobo

Hotuna da bidiyon matashiyar basarakiya da ta karya tarihin shekara100 na kabilar Urhobo

  • Matashiyar mai sharhin labaran wasanni, Suo Chapele, ta sanar da nadin sarautar gargajiya da aka yi mata a kasar Urhobo
  • Kamar yadda matashiyar ta sanar, ta karya tarihin sama da shekaru dari inda ba a baiwa diya mace gadon sarautar mahaifin ta
  • Suo ta ce 'yan uwanta, dangi da dattawa sun ga ta dace duk da akwai 'ya'ya maza a gidansu amma sarki ya nada ta Okugbe ta masarautar Udu

Mai sharhin labaran wasanni, Suo Chapele, ta bayar da labarin yadda ta karya wani babban tarihin shekaru dari na al'adar kasar Urhobo yayin da ta samu sarauta.

A wallafar da ta yi a shafinta na kafar sada zumunta na Instagram, Suo ta sanar da yadda sarakunan Urhobo ba su bai wa diya mace gadon sarautar mahaifin ta amma 'yan uwanta da dattawa suka ga ta dace da sarautar.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Miyagun Yan bindiga sun kuma sace wani Sarki a Najeriya

Hotuna da bidiyon matashiyar basarakiya da ta karya tarihin shekara100 na kabilar Urhobo
Hotuna da bidiyon matashiyar basarakiya da ta karya tarihin shekara100 na kabilar Urhobo. Hoto daga @officialsuo
Asali: Instagram

Wallafar shafin ta

A yayin wallafa bidiyon ta sanye da kayan sarautarsu ta gargajiya, ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A kusan shekaru dari, sarakunan Urhobo ba su bai wa 'ya mace gadon sarautar mahaifin ta ballantana idan akwai 'ya'ya maza. A yau, jama'a ta, 'yan uwa, da dattawa sun ga cancanta ta.
"A yau, masarautar Udu da ke kasar Urhobo ta ga na dace. A yau sarki na ya mika min sarautar mahaifina: Ina gabatar muku da Olorogun Avwerosuoghene Chapele, Okugbe ma'ana mai tabbatar da hadin kai da zaman lafiya ta masarautar Udu."

Ga hotunan basarakiyar:

Martanin jama'a

Tuni ma'abota amfani da kafar sada zumuntar ska fara taya matashiyar murna. Ga tsokacin da suka yi:

@kemkemcrypt: "Na taya ki muran, a yanzu za mu iya kiran ki da babbar manazarciya."
@prettyfunmmie: "wannan murmushin sihirtacce ne."

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya ja kunne kan siyasantar da rashin tsaro, ya ce yunwa ba ta san addini ba

@isiokpobabe_: "Ina matukar taya ki murna 'yam mata. Baba zai yi alfahari da ke

Jaruma Rahama Sadau ta caccaki gwamnatin Buhari kan hauhawar rashin tsaro

A wani labari na daban, fitacciyar jarumar fina-finai ta Najeriya, Rahama Sadau, ta caccaki gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari kan yadda ta gaza shawo kan matsalar tsaro da ta kazanta a arewa da Najeriya baki daya.

Sadau wacce ta wallafa caccakar a shafinta na Instagram a ranar Litinin, ta ce "har sai gwamnati ta tashi tsaye kan lamarin, ko kuma za a iya kai 'yan Najeriya bango har su yi bore".

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng