Sarkin Musulmi ya ja kunne kan siyasantar da rashin tsaro, ya ce yunwa ba ta san addini ba

Sarkin Musulmi ya ja kunne kan siyasantar da rashin tsaro, ya ce yunwa ba ta san addini ba

  • Sarkin musulmi, Sa’ad Abubakar ya ja kunnen shugabannin addinai da na siyasa akan siyasantar da batun rashin tsaron da ya addabi kasar nan
  • Kamar yadda ya sanar, yunwa ba ta san addini ko kabila ba, za ta cigaba da yawaita sakamakon rashin tsaron da yayi katutu a yankunan kasar nan
  • Duk da kazantar rashin tsaro a kasar nan, Sarkin Musulmin ya ce yana sa ran cewa wata rana za a shawo kan matsalar kasar nan

Sarkin Musulmi, Sa’ad Abubakar, ya ja kunne akan kada shugabannin addinai da 'yan siyasa su mayar da matsalar tsaron Najeriya ta siyasa.

Ana ta samun karin rashin tsaro, ta’addanci da sauran ayyukan assha yayin da ‘yan bindiga da sauran ‘yan ta’adda su ke cin karensu babu babbaka a arewa maso yamma, arewa maso gabas da sauran bangarori.

Kara karanta wannan

Matasan Arewa ga Obasanjo: Kai dai ba ka da bakin sukar gwamnatin shugaba Buhari

Akwai mutane da dama da aka halaka, aka yi garkuwa da su sannan wasu aka yi musu fyade, Channels TV ta ruwaito hakan.

Sarkin Musulmi ya ja kunne kan siyasantar da rashin tsaro, ya ce yunwa ba ta san addini ba
Sarkin Musulmi ya ja kunne kan siyasantar da rashin tsaro, ya ce yunwa ba ta san addini ba. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Akwai jihohin da har dakatar da kafafen sadarwarsu aka yi saboda matsalar rashin tsaro duk a arewa maso yamma, Channels TV ta ruwaito hakan.

Yayin magana a Abuja, a wani taro na kawo gyara akan matsalar tsaro, sarkin musulmi ya ce kada a siyasantar da matsalar tsaro a kasar nan.

“Wajibi ne mu lura don kada mu siyasantar da rashin tsaro saboda yunwa bata san siyasa ko addini. Kowa ya na korafi kan yunwa a kasa kuma da gaske ne," Sultan yace.

"Daya daga cikin manyan matsalolin da muka sani shi ne mayunwaci dama fusatacce ne. Akwai matukar amfani mu sani cewa, a duk lokacin da muka hadu a matsayin shugabannin addini ko na siyasa, dole ne mu duba abu daya. Mu hada kanmu a matsayinmu na mutane."

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Hukumar DSS ta ja kunnen Malaman addini da Sarakuna a kan sakin bakinsu

Ya kara da koka wa kan yawan kashe-kashen da ake fuskanta a kasar nan inda yayi kira ga gwamnati da ta samar da daidataccen muhalli ga 'yan Najeriya domin su yi addinansu.

Duk da kazantar rashin tsaro, Abubakar ya ce yana sa ran Najeriya za ta iya shawo kan matsalolin rashin tsaron ta.

A matsayin hanyar cigaba, Sarkin Musulmin ya yi kira ga 'yan Najeriya da su hada kai ba tare da duban banbancin siyasa, addinai da kuma kabila ba.

Sarkin Musulmi ya koka, yace 'yan ta'adda na kashe jama'ar arewa kowacce rana

A wani labari na daban, sarkin musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar ya koka akan yadda ‘yan bindiga a kullum suke halaka mutane a arewacin Najeriya musamman a arewa maso yamma duk da dai ba kowanne kisa ake fadi ba.

Wannan ya biyo bayan kiran da Sultan din ya yi wa Kiristoci akan wani razanarwar da wasu da ba a san su ba su ka yi musu, inda suka ce su dakata da zuwa coci a jihar Zamfara ko a halaka su, Tribune Online ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya za su fi ganin amfanin Buhari bayan ya sauka daga mulki, Gwamnan arewa

Yayin jawabi a taron wata ukun karshen shekarar 2021 na kungiyar hadin kan addinai (NIREC) mai taken, ‘Jami’an tsaro da zaman lafiya a Najeriya’ wanda Sultan din ne shugaban NIREC, ya ce babu ranar da za ta wuce ba a halaka mutane ba a arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng