Gwamnatin Sokoto za ta gurfanar da matar jami'in kwastam da ta kusa halaka diyar kishiya
- Uwargidan gwamnan jihar Sokoto, Dr Mariya Tambuwal, ta bayar da umarnin bincike tare da bin hakkin matashiyar da kishiyar uwa ta nema halakawa
- Kamar yadda dakta Mariya ta sanar, za a bibiyi wadanda ke da hannu a neman kashe matashiyar ko da kuwa mahaifiyar ta bata gidan mahaifin
- A cikin kwanakin nan ne wasu bidiyo na yadda kishiyar mahaifiyar matashiya Hafsat ta farfasa mata jiki tare da kakkarya ta da tabarya
Sokoto - Matashiyar yarinya mai shekaru 17 wacce kishiyar mahifiyar ta kusa halakawa a jihar Sokoto za ta samu adalcin da ya dace ta hannun matar Gwamna Aminu Waziri Tambuwal, mariya Tambuwal.
Uwargidan gwamnan jihar, Mariya Tambuwal, ta umarci kwamishinan shari'a na jihar da ya bincike lamarin tare da gurfanar da duk wanda ke da hannu a ciki.
Matashiyar yarinyar, diyar tsohon Comptroller na hukumar kwastam kuma Ajiyan Kabi, Alhaji Abdullahi Argungun ce.
21st century chronicles ta ruwaito cewa, kishiyar mahaifiyar Hafsat ta yi mata dukan kawo wuka da tabarya kan zarginta da sata da kuma rashin sallah tare da sauran laifuka.
Sakamakon mugun dukan, yarinyar ta kakkarye tare da samun miyagun raunika, 21st Century Chronicles ta ruwaito.
Sai dai, uwargidan Tambuwal ta yi kira ga antoni janar na jihar Sokoto kuma kwamishinan shari'a, Sulaiman Usman, da ya tsananta bincike kan lamarin tare da gurfanar da dukkan masu hannu a ciki.
"Ba shakka dole ne iyaye su kula da 'ya'yansu, saboda za su amsa tambayoyi gaban Allah. Hukumomi suna da hakkin yin duk abinda ya dace wurin maganin iyayen da basu daukar nauyinsu.
"Abinda miyagun suka yi abun kunya ne kuma za a tabbatar da cewa an bi mata hakkinta ko da kuwa mahaifiyar ba ta gidan," Dr Mariya tace.
Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar
A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya wanda ya je yin hidimar kasa ya bukaci auren daya daga cikin sojojin da ya taras a sansanin masu hidimar kasa a jihar Kwara.
A wani guntun bidiyo wanda @instablog9ja su ka wallafa a Instragram, matashin ya durkusa har kasa sannan ya sa wa sojar zobe a yatsanta. Nan da nan mutane su ka fara ihu.
Mutane da dama sun dinga tsokaci da mamakin bajintar wannan jarumi. Sauran matasan da su ke cikin sansanin sanye da kayan masu hidimar kasa sun yi ta murna yayin da sojar ta rufe bakinta cike da murna.
Asali: Legit.ng