Da Dumi-Dumi: Zazzabin Lassa ya hallaka likitoci da wasu mutane a Nasarawa
- Bayan tabbatar da cutar zazzabin Lassa mai kisa ta barke a Nasarawa, NCDC ta sanar da mutanen da zazzabin ya kashe
- Hukumar yaƙi da yaɗuwar cututtuka ta ƙasa tace mutum biyu suka mutu cikinsu har da wani kwararren likita
- Kazalika zazzabin ya sake kama wani likita kuma tuni aka ɗauke shi zuwa Abuja domin kulawa da lafiyarsa
Nasarawa - Aƙalla mutum biyu ne aka tabbatar da sun mutu biyo bayan ɓarkewar zazzaɓin Lassa a jihar Nasarawa.
Dailytrust ta ruwaito cewa mutum ɗaya daga ciki waɗan da aka tabbatar da mutuwarsu, kwararren likita ne.
Bayn shi kuma sai wata mata mai juna biyu, amma an samu wani likita da ya kamu zazzabin yanzu haka yana kwance yan karban kulawa.
A wata sanarwa mai ɗauki da sa hannun darakta janar na hukumar NCDC, Ifedayo Adetifa, waɗan da suka mutu sune mace mai juna biyu da likita.
The Cable ta rahoto wani sashin sanarwan yace:
"A ranar 8 ga watan Disamba, hukumar NCDC ta sanar da mutuwar mutum biyu dake fama da zazzabin Lassa. Na farko wata mace ce mai juna biyu a jihar Nasarawa. Na biyu kuma likita ne dake duba mara lafiya, wanda daga baya aka dawo da shi Abuja don kula da shi."
"Daɗin daɗawa, an sake gano wani likita ɗauke da cutar ta zazzaɓin Lassa, kuma yanzu haka yana karban kulawa a Asibitin Abuja."
"Ma'aikatar lafiya ta jihar Nasarawa da gudummuwar hukumar NCDC ta fara gudanar da bincike musabbabin yaɗuwar zazzabin da kuma gano iyakar inda ta shiga."
Wane mataki hukumomi ke ɗauka?
Hukumar ta bayyana cewa tana bibiyar mutanen da aka tabbatar da sun kamu da zazzaɓin lassa tun bayan ɓarkewarta a jihar Nasarawa.
"Mun bude cibiyoyin gaggawa na zazzaɓin Lassa a jihar da abun ya shafa da kuma Abuja. NCDC na mika ta'aziyya ga iyalan masara lafiya da ma'aikatan lafiya, waɗan suka rasa ransu."
A wani labarin na daban kuma Gwamnonin Arewa ta Gabas sun shiga ganawar sirri a jihar Yobe
Gwamnonin jihohi shida da suka haɗa yankin arewa maso gabas sun shiga ganawar sirri karo na shida a Damaturu, babban birnin jihar Yobe.
Taron ya samu jagorancin shugaban gwamnonin kuma gwamnan Borno, Babagana Zulum kuma gwamna Mala Buni na Yobe ya karbi bakuncin shi.
Asali: Legit.ng