Rashin tsaro: Hukumar DSS ta ja kunnen Malaman addini da Sarakuna a kan sakin bakinsu

Rashin tsaro: Hukumar DSS ta ja kunnen Malaman addini da Sarakuna a kan sakin bakinsu

  • Jami’an DSS masu fararen kaya sun yi kira ga al’ummar kasar nan su guji siyasantar da lamarin tsaro
  • Hukumar DSS ta fitar da jawabi na musamman jiya, ta na jan hankalin mutane da su iya bakinsu
  • Sanarwar da hukumar ta fitar ya hada da jan-kunnen malaman addini da shugabanni na gargajiya

Abuja - Hukumar DSS masu fararen kaya a Najeriya, ta ja-kunnen mutane da su yi wa bakinsu linzami, yayin da ake fama da matsalolin rashin tsaro.

BBC Hausa ta fitar da rahoto a ranar Talata, 14 ga watan Disamba, 2021 cewa an gargadi al’ummma, daga ciki har da malamai da masu sarauta.

Jan-kunnen ya fito ne daga bakin mai magana da yawun bakin hukumar DSS na kasa, Peter Afunanya.

A cewar Peter Afunanya, DSS ta gano cewa wasu ‘yan siyasa da idanunsu ya rufe wajen neman mulki su na ruruta wutar rikici saboda cin manufar siyasa.

Kara karanta wannan

Nasara: Sojoji sun ragargaji sansanin dan bindiga Bello Turji, sun hallaka da dama

A dalilin haka ne DSS ta gargadi masu sarautar gargajiya da malaman addini da ake jin maganarsu, su kauracewa duk wani abin da ya saba doka.

Sarakuna
Sarakunan gargajiya a Aso Villa Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Rahoton yace sanarwar ta fito ne a yayin da ake kuka a kan yadda sha’anin tsaro ya tabarbare. Lamarin ya fi kamari a wasu jihohi na Arewa maso yamma.

Sanarwar da DSS ta fitar a jiya

"Tuni masu irin wannan aƙida sun fara siyasantar da matsalar rashin tsaro a wasu sassan ƙasar nan saboda wasu dalilai na son kansu.”
"Da yawansu na amfani da halin da aka shiga domin jawo rabuwar kan al’umma, da neman suna da ko kuma sanya ƙasar cikin matsala."
"Ana neman jagororin al’umma irinsu malamai da sarakunan gargajiya su iya bakinsu, kuma su guji kalamai masu tunzura jama’a.” -DSS

Kara karanta wannan

Fadar Shugaban kasa ta jero tulin nasarorin Shugaba Buhari yayin da ya cika shekara 79

A jawabin da ta fitar a Abuja, DSS ta gargaɗi duk masu wannan danyen aiki, su sake tunani.

Haka zalika hukumar tsaron tayi kira da babbar murya ga ‘yan siyasa su tsaya a kan doka, su guji yin abin da zai tunzura al’umma yayin da ake hango zaben 2023.

Masoyan Muhammadu Buhari sun ragu

A makon nan ku ka ji cewa garkuwa da mutane ya na kara kamari, inda aka ji cewa an yi awon gaba da mutane dama a titin Zaria zuwa Kaduna, a jihar Kaduna.

Dakarun Sojojin Najeriya sun yi kokarin kubuto wasu da ‘Yan bindigan suka dauke. Ana zargin hakan suke jawo farin jinin Muhammadu Buhari yake raguwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng