Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar

Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar

  • Daga zuwa bautar kasa, wani dan Najeriya ya hadu da soja wacce ya bukaci ta aure shi don su ci gaba da rayuwa tare
  • Nan da nan masu yi wa kasa hidima su ka dinga ihu da mamakin kwarin guiwarsa akan neman auren soja
  • Bidiyon yadda lamarin ya auku ya janyo tsokaci iri-iri daga mutane da dama, lamarin ya auku ne a jihar Kwara

Kwara - Wani matashi dan Najeriya wanda ya je yin hidimar kasa ya bukaci auren daya daga cikin sojojin da ya taras a sansanin masu hidimar kasa a jihar Kwara.

A wani guntun bidiyo wanda @instablog9ja su ka wallafa a Instragram, matashin ya durkusa har kasa sannan ya sa wa sojar zobe a yatsanta. Nan da nan mutane su ka fara ihu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun sake kai mummunan hari kan matafiya a hanyar Kaduna-Abuja

Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar
Bidiyon matashi mai bautar ƙasa ya na neman auren soja a sansanin NYSC ya ƙayatar. Hoto daga @Instablog9ja
Asali: Instagram

Mutane da dama sun dinga tsokaci da mamakin bajintar wannan jarumi.

Sauran matasan da su ke cikin sansanin sanye da kayan masu hidimar kasa sun yi ta murna yayin da sojar ta rufe bakinta cike da murna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yanzu haka an samu fiye da mutane 1,700 da su ka dinga tsokaci karkashin bidiyon.

Martanin jama'a

Legit.ng ta tattaro wasu tsokacin jama’a:

@dancole_me ta ce:

“Kyakkyawa ce...kamar in zo in nemi aurenta.”

@sir_eltee ya ce:

“Yaron nan ya yi amfani da makwanni ukunsa da kyau. Nawa kuwa buya na dinga yi don ban yi komai ba sai cin abinci. Ina taya su murna.”

Papizzy_dxp ya ce:

“Yarinyar nan zane shi za ta yi.”

@iamsamueleto ya ce:

“Yaron nan jarumi ne fah.”

BaAmurkiya mai digiri 4 ta gangaro Afrika, ta yi wuff da dan achaba, tace hadin Ubangiji ne

Kara karanta wannan

Jigon gwamnati ya bayyana yadda kyankyaso mai rai ya zauna a kunnensa na tsawon watanni

A wani labari na daban, Carey Joy da Albert Wanyonyi bayani ne gamsasshe kan cewa soyayya ruwan zuma ce.

Carey wacce ta je mishan kasar Kenya ta aure Wayonyi, wanda da kyar ya ke iya bayani da turanci tunda a makarantar firamare ya tsaya da karatu.

A tattaunawar da aka yi da shi a bayan, Wayonyi ya ce ya fada kaunar matarsa duk da cewa akwai kalubale da banbancin da suke da shi na yare.

A yayin jawabi yayin da gidan talabijin din TV 47, mahaifiyar kyawawan yara biyun ta bayyana cewa ta na da digiri hudu a fannoni daban-daban. Daya daga ciki na tattalin arziki ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng