Likita ya bayyana larurar da ta sa Zakzaky da Mai dakinsa su ke neman barin Najeriya

Likita ya bayyana larurar da ta sa Zakzaky da Mai dakinsa su ke neman barin Najeriya

  • Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da mai dakinsa, Malama Zeenah Zakzaky, sun kamu da cututtuka iri-iri
  • Likitansu, Dr. Abubakar Yahaya yace wannan ya sa suke bukatar fita zuwa kasar waje domin a duba su
  • Dr. Yahaya yake cewa a shekarar 2018, Shugaban IMN, Zakzakya ya samu matsalar shanyewar jiki

Abuja - Jaridar Punch ta rahoto likitan gidan malamin addinin, Dr. Abubakar Yahaya ya na cewa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da iyalinsa ba su da lafiya.

Dr. Abubakar Yahaya yace shehin malamin da uwar gidarsa duk su na dauke da cututtuka 11, don haka suke neman damar zuwa asibiti a kasashen ketare.

A cewar likitan, hujjoji sun tabbatar da cewa El-Zakzaky da uwar ‘ya ‘yansa wanda aka tsare su tare, su na fama da matsalolin rashin lafiya a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Ku daina sa ran samun wani abin a mulkin Shugaba Buhari – Obasanjo ga mutanen Najeriya

Likitan ya musanya ikirarin da gwamnatin Muhammadu Buhari tayi ta bakin Abubakar Malami SAN na cewa babu abin da ya nuna Zakzaky bai da lafiya.

Likitan yace gwaje-gwajen da aka yi kamar yadda aka saba yi tun da Zakzaky ya samu shanyewar jiki a 2018, ya nuna yana bukatar zuwa asibiti.

Zakzaky
Sheikh Ibrahim El-Zakzaky Hoto: www.bbc.com
Source: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Menene sakamakon gwajin da aka yi?

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba, 2021, Dr. Yahaya yace an yi wa malamin gwajin a wasu asibitoci da aka yarda da su.

Sakamakon ya nuna Zakzaky da matarsa, su na dauke da wasu cututtuka masu hadarin gaske.

“Gwajin da aka yi masu na karshe ya tabbatar da cewa akwai cututtuka har 11 masu hadari da suke damun Sheikh Zakzaky har zuwa yanzu.” - Dr. Yahaya

Jerin cututtukan da Zakzaky ke fama da su

Daga cikin cuttukan da likitan ya lissafo, akwai cutar zuciya ta Ischaemic, ventricular hypertrophy, shanyewar bangaren jiki, da gocewa ta spondylosis.

Kara karanta wannan

Matasa Sun Fita Gari Sunyi Zanga-Zanga Kan Yawaitar Kashe-Kashe a Arewa

Sauran cuttukan su ne ciwon idanu na anophthalmia da glaucoma, prostate hypertrophy da yawan sinadaran Lead da cadmium a jikin malamin da matarsa.

Rahoton yace ita ma Zeenat Zakzaky ta na dauke da wadannan cututtuka baya ga ciwon gwiwa, ciwon ciki, yawan hawan jini da bugun zuciya da ciwon cibiya.

Sambo Dasuki, Tinubu da Akande a 2011

Kwanan nan ake jin cewa Kanal Sambo Dasuki ya nemi alfarma wajen su Bola Tinubu da Bisi Akande cewa su ba Muhammadu Buhari tikitin takara a zaben 2011.

A lokacin da aka gwabza da Goodluck Jonathan a 2011, Ribadu ya yi niyyar ya janyewa Buhari. Bayan Buhari ya samu mulki a 2015 ne ya daure Sambo Dasuki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng