Karin Bayani: Yan ta'addan ISWAP sun gwabza da Mafarauta a Jihar Borno
- Rahoto ya bayyana cewa wasu da ake zargin mayakan ISWAP ne sun kai hari kauye a kudancin jihar Borno
- Wata majiya ta bayyana cewa mafarauta a yankin kauyen sun tarbi yan ta'addan, inda suka yi ɗauki ba daɗi
- Mamban kungiyar jami'an sa'kai, CJTF, ya bayyana cewa mayakan ISWAP sun ci karfin mafarautan sun shiga cikin ƙauyen
Borno - Wasu yan ta'adda da ake zargin mayakan kungiyar ISWAP ne na can sun farmaki wani kauye a kudancin Jihar Borno, kamar yadda Dailytrust ta rahoto.
Yan ta'addan sun farmaki kauyen Shallangba wanda ke kusa da Debiro a karamar hukumar Hawul, jihar Borno.
Sai dai rahotanni sun bayyana cewa mafarauta yan sa kai sun tarbi yan ta'addan, kuma sun fafata da juna yayin harin.
A cewar wata majiya, yan ta'addan sun kai hari ƙauyen a kan motoci, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi yayin da mutanen kauyen suke kokarin tserewa zuwa cikin jeji.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mamban tawagar jami'an tsaron sa kai (CJTF) yace yan ta'addan sun fi karfin mafarautan, yanzu haka suna cikin ƙauyen.
A ranar Lahadi da maraice, wasu yan ta'adda suka kai hari ƙauyukan Debiro, wanda ya haɗa iyaka da kananan hukumomin Biu da Hawul na jihar Borno.
A kwanakin bayan nan dai, yan ta'addan dun matsa da kai hare-hare jihar Borno, inda a wani harin suke sace matafiya.
A wani labarin na daban kuma Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana abinda Buhari ke yi domin kawo karshen kalubalen tsaro a faɗin Najeriya
A kullum shugaba Buhari sai ya yi maganar mutanen da ake kashewa tare da yi musu addu'a, inji fadar shugaban kasa.
Malam Garba Shehu, a wata sanarwa da ya fitar, yace shugaba Buhari yana damuwa fiye da tunani kan halin rashin tsaro da ake ciki.
Asali: Legit.ng