Kasashen musulman duniya sun yi Allah-wadai da babbaka matafiya a Sokoto
- Kungiyar hadin kan kasashen muslami ta duniya ta yi Allah wadai da hallaka 'yan Najeriya a yankin jihar Sokoto
- Kungiyar ta mika jaje ga shugaban kasa da ilahirin 'yan Najeriya kan wannan mummunan lamari da ya afku
- Hakazalika, kungiyar ta kuma bayyana addu'arta ga wadanda lamarin ya rutsa dasu, tare da jajantawa iyalansu
Babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC), Hissein Taha, ya bayyana kakkausar suka kan harin ta’addanci da aka kai kan wata motar bas din fasinja a Arewa maso yammacin Najeriya a ranar Talata 7 ga watan Disamba, 2021.
Idan baku manta ba, a makon jiya ne wasu 'yan bindiga suka tare wata mota, suka banka mata wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 23, kamar yadda TheCable ta rahoto.
Harin ya yi sanadin mutuwar mutane akalla 30 tare da jikkata wasu da dama, Daily Nigerian ta ruwaito.
Babban sakataren ya bayyana harin a matsayin zalunci daga matsorata sannan ya bayyana jaje daga OIC ga gwamnati da al’ummar Najeriya a wannan mawuyacin lokaci.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya jajanta wa wadanda wannan bala’i ya rutsa da su, tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin gaggawa.
Sakataren ya kuma jaddada matsayar kungiyar ta OIC a kan yin Allah-wadai da kowane nau'i na ta'addanci da tsattsauran ra'ayi.
Sheikh Gumi: 'Yan bindiga sun sace yayana, sun kashe dan direban gidanmu
A wani labarin, shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa shi ma ya sha fama da hare-haren ‘yan bindiga da ke addabar arewa.
Ya ce an yi garkuwa da yayansa kuma sai da ya biya kudin fansa domin a sake shi.
Malamin na Kaduna ya bayyana hakan ne a wata hira da jaridar Premium Times ta wallafa a ranar Lahadi, 12 ga watan Disamba.
Asali: Legit.ng