Yanzu-Yanzu: Buhari ya nemi duniya tasa Amurkawa a addu'a saboda mutuwar mutane 100
- Shugaba Buhari na Najeriya ya bayyana jimami da samun labarin mutuwar wasu mutane a kasar Amurka
- A cewar Buhari, ya kamata duniya su hadu su yi wadanda lamarin ya shafa addu'a tare da bayyana jimaminsu
- Shugaban ya bayyana haka ne ta bakin mai bashi shawari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina a yau Lahadi, 12 ga watan Disamba
Abuja - Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa da jin labarin abinda ya faru a Amurka a makon da ya gabata.
Rahotannin da muke samu daga jaridar The Guardian sun bayyana cewa, an samu afkuwar wata mummunar guguwa a kasar Amurka, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane sama da 100.
Da yake mayar da martani kan wannan mummunan lamari, shugaba Buhari ya ce, ya kamata duniya ta sanya wadanda lamarin ya shafa a addu'o'insu.
A cewar wata sanarawa da Legit.ng Hausa ta samo daga mai ba shugaban shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya bayyana yadda shugaban ya kadu da jin labarin.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Femi Adesina ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta wa gwamnati da al’ummar kasar Amurka sakamakon mummunar guguwar da ta barke a jihohi shida, inda ta yi barna tare da yin kisa.
Da yake mayar da martani game da bala'in da aka fara yadawa a duniya tun daga ranar Juma'a, Shugaba Buhari ya ce:
"Rushewar garuruwan baki daya, barnata gidaje, makarantu, asibitoci, kasuwanni da sauran ababen more rayuwa a matakin da ba a ta ba ganin irinsa ba abin takaici ne matuka."
"Muna mika babban juyayinmu zuwa ga duk wadanda abin ya shafa, da gwamnati da jama'ar Amurka."
Adesina ya kara da cewa, shugaban ya bukaci ‘yan kasar da su hada kai da sauran kasashen duniya wajen yi wa wadanda suka rasu addu’a da kuma baiwa sauran wadanda abin ya shafa da iyalansu lafiya a wannan mawuyacin lokaci.
Shugaba Buhari ya yi sammako, ya sauka a filin jirgin sama na jihar Legas
A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka jihar Legas a yau Alhamis, Channels Tv ta ruwaito.
Buhari ya sauka a masaukin shugaban kasa na filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammed da ke Legas da sanyin safiyar yau Alhamis.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da wasu jami’ai ne suka tarbi shugaban a filin jirgin.
A yayin ziyarar, ana sa ran Buhari zai kaddamar da jiragen ruwa da jirage masu saukar ungulu tare da halartar taron kaddamar da littafin tsohon shugaban jam'iyyar APC, Bisi Akande, a cewar Independent.
Asali: Legit.ng