Tsaro: Ina kira da Buhari ya tashi tsaye, jama’a kuma su dage da addu’a, Sheikh Bala Lau
- Shugaban kungiyar Izalah (Jibwis) ya yi kira ga sshugaba Buhari ya kara kaimi wajen magance matsalar tsaro
- Ya kuma yi kira ga jama’a da a dage da addu’a domin babu abun da ya gagari Allah
- Shugaban yayi kira da babban murya ga jami’an tsaro da su samo sabbin dabaru yakin da yan ta'adda
Kungiyar Izalatul Bid'a wa iqaamatus Sunnah (JIBWIS) tayi kira ga gwamnatin tarayyar da ta kara kaimi wajen dakile matsalar tsaro da ya addabi arewacin kasar, musamman jihohin Sokoto, Zamfara, Niger, Kaduna da jihar Katsina.
A jawabin da Ibrahim Baba Suleiman ya saki a madadin kungiyar a shafin JIBWIS na Facebook, ya bayyana cewa shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya bayyana hakan a tattaunawa da yayi da ‘Yan jaridu a ofishinsa dake birnin Abuja.
Shugaban yayi kira da babban murya ga jami’an tsaro da su samo sabbin dabaru domin kawo karshen zubar da jinin al’umma tare da murkushe’yan ta’adda a wannan yanki.
Ya kara da cewa wadannan‘Yan ta’adda basu fi karfin jami’an tsaron Naijeriya ba, amma abun kullum Sai gaba-gaba yakeyi, ana ta zubar da jinin al’umma wadanda basuji ba basu gani ba.
A cewarsa, shehin malamin yace;
“Allah ta’ala ya halicci bayi da falalarsa ya bayyana musu daidai daga kuskure, Allah ya haramta zalunci wa kansa, kuma ya sanya ta haramun a tsakanin bayinsa, sannan yace kada kuyi zalunci, domin samar musu da rayuwa mai nagarta."
"Hakika Al'amarin Amana na jagoranci wajibine Al'umma su sani Musulunci yayi fayyacecciyar bayani akayi, wanda yake wajibine Shugaba ya tsare lafiyar Al'umma, rayukansu da dukiyoyinsu. Kuma tabbas Allah zaiyi Hisabi akan wadannan”.
Jama’a a dage da addu’a domin babu abun da ya gagari Allah
Shugaban Izalan ya sake kira da jama'ar Arewa suma su kara kaimi wajen addu'a saboda komai na bukatar addu'a.
Yace:
"Dan haka ina kira ga jama’a da mu kara hakuri, muyi ta addu’oi a masallatai da wuraren ibadu da tarurrukan addini, sannan muyi hakuri insha Allah, Allah zai dube mu da idon rahama ‘’Allah taala yace "lalle tare da tsanani akwai sauki"
Sayyiduna umar yace tsanani bai taba rinjayar sauki biyu ba'. Annabi s.aw yace ' kuyi hakuri har sai kun iskeni a bakin tabki' Lalle Allah yana tare da masu hakuri, kuma baya tauye ladan masu hakuri.
Allah ya kawo mana karshen‘Yan ta’adda da duk wani mai hannu a cikin wannan zalunci. Amin"
Asali: Legit.ng