Wata sabuwa: SSS ta gayyaci daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zanga a Arewa
- A yau ne mutanen Arewa suka fito suka bayyana rashin amincewarsu ga yadda ake kashe-kashe a yankin Arewacin Najeriya
- An gudanar da zanga-zangar nuna kin jinin kashe-kashen a jihohin Arewa daban-daban, ciki har da babban birnin tarayya Abuja
- Hukumar SSS ta gayyaci daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar domin tattauna wasu batutuwa
Kano - Hukumar tsaro ta farin kaya (SSS), ta gayyaci daya daga cikin wadanda suka shirya zanga-zangar #NoMoreBloodShed a Kano, Zainab Nasir Ahmed.
An shirya zanga-zangar ne domin jawo hankalin gwamnati kan yadda matsalar tsaro ke kara ta’azzara a Arewa, biyo bayan mummunan kisan da aka yi wa matafiya sama da 42 a wata motar a Sokoto.
Zainab Ahmed ta tabbatar wa Daily Nigerian gayyatar, inda ta ce tana kan hanyarta ne domin karrama wannan gayyata.
A cewarta:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Yanzu suka kira ni a waya suka shaida min cewa ana bukatar gani na a ofishin DSS sakamakon zanga-zangar da muka yi a yau. Ina hanyar zuwa don girmama gayyatar a matsayina na 'yar kasa mai bin doka."
A safiyar yau ne dai wasu matasa suka mamaye titunan wasu garuruwan Arewa saboda nuna kin jinin kashe-kashen da ake yi a yankin.
A halin yanzu Najeriya na fama da matsalar rashin tsaro, ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda sun zafafa kai hare-hare a Arewacin kasar duk da kokarin da gwamnati tace tana yi don dakile hare-haren.
Masu zanga-zangar wadanda ke dauke da alluna, sun shirya zanga-zangar ne a lokaci guda a jihohin Kano, Bauchi, Zamfara, Sokoto da babban birnin tarayya Abuja.
Masu zanga-zangar suna rera wakokin zaman lafiya, sun kuma yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da su kara nuna sha'awarsu ga magance matsalar rashin tsaro.
Bayan zanga-zangar ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tura tawagar jami’an tsaro zuwa jihohin Katsina da Sokoto da ke fama da rikici a kwanakin nan.
Shugaban ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Bayan kona fasinjoji da ransu, 'yan bindiga sun sake zubar da jini a wani gari a Sokoto
A wani labarin, wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun afka kauyen Kurawa da ke karamar hukumar Sabon Birni a jihar inda su ka halaka mutane uku, Daily Trust ta ruwaito.
Harin ya auku ne bayan sa’o’i kadan da gwamnan jihar, Aminu Tambuwal ya kai ziyara yankin.
Tambuwal ya je ta’aziyya gami da jaje ne ga ‘yan uwan wadanda mummunan lamarin ya ritsa da su inda ‘yan bindiga a daidai titin Sabon Birni-Isa su ka babbaka su kurmus ranar Litinin.
Asali: Legit.ng