An yi jana'izar Kwamishanan Kimiyar jihar Katsina da aka kashe a gidansa
- An kai marigayi kwamishanan Kimiya da Fasaha na jihar Katsina makwancinsa
- Manyan Malamai da jagororn siyasan tarayya da jihar Katsina sun halarci taron jana'izar
- An gudanar da addu'o'in Allah ya jikansa kuma ya karbi shahadarsa
Katsina - An gudanar Sallar Jana'izar Kwamishsnan Kimiya da Fasahan jihar Katsina, Dr Nasir Rabe, karkashin jagorancin Limamin Masallacin Katsina GRA, Dr Aminu Abdullahi Yammawa.
An bizne marigayin ne a makabartan Gidan Dawa bayan Sallar Jana'izar, rahoto DailyTrust.
Wasu suka hallaka marigayin ranar Laraba cikin gidansa.
Wadanda suka halarci Jana'izar sun hada da Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello MAsari da tawagar gwamnatin tarayya karkashin jagorancin mai bada shawara kan lamuran tsaro, Manjo Janar Babagna Monguno.
Sauran sune Sifeto Janar na yan sanda, Usman Alkali Baba; Shugaban hukumar DSS, Yusuf Magaji Nasir; Shugaban hukumar NIA, Ahmed Rufa’I Abubakar da MAnjo Janar Samuel Adebayo.
Sakon Gwamnatin tarayya
Shugaban tawagar Gwamnatin tarayya yace Shugaban kasa ne ya tura shi jajantawaa Gwamnatin jihar Katsina da iyalan mamacin.
A cewarsa:
"Shugaban kasa ya umurceni in jagoranci wannan tawaga a madadinsa bisa abin takaicin da ya auku ga kwamishana a jihar."
"Yanayin yadda abin ya faru, yan sanda basu kammala bincike ba. Amma Shugaban kasa ya yi imanin cewa Hukumar yan sandan Najeriya zasu damke wadanda suka aikata wannan abu kuma a hukuntasu."
Yadda aka kashe Kwamishanan Kimiyar jihar Katsina, Majiya
Hukumar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar Kwamishann Kimiya da Fasahan jihar Katsina, Dr Rabe Nasir, wanda aka kaiwa hari gidansa ranar Alhamis.
Wata majiya ta kusa da mamacin a rukunin gidajen Fatima Shema dake Katsina tace:
"An gano gawarsa ne lokacin da daya daga cikin masu girkin gidan ya shiga dakin Dr Rabe Nasir kuma ya kwankwasa kofa amma bai amsa ba. Bayan ganin jini sai ya kira jama'a."
"Da wuri mai girkin ya sanar da dogarin kwamishanan wanda ya shiga ya ga an boye gawar mamacin cikin bayin dake dakinsa."
Asali: Legit.ng