Yadda aka kashe Kwamishanan Kimiyar jihar Katsina, Majiya
- Wasu makasa sun hallaka kwamishanan gwamnan jihar Katsina a cikin gidansa dake cikin birnin Katsina
- Majiya dake kusa da mamacin ta bayyana cewa tun ranar Laraba aka kashe shi
- Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ziyarci gidan da aka kashe kwamishinan
Hukumar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar Kwamishann Kimiya da Fasahan jihar Katsina, Dr Rabe Nasir, wanda aka kaiwa hari gidansa ranar Alhamis.
Kwamishanan yan sandan jihar, Sanusi Buba, wanda ya ce an kashe mamacin a daren Laraba a dakinsa amma ba'a gano gawarsa ba sai ranar Alhamis.
Ya kara da cewa an kaddamar da bincike, kuma an kama mutum daya.
A cewar Tribune, wata majiya ta kusa da mamacin a rukunin gidajen Fatima Shema dake Katsina tace:
"An gano gawarsa ne lokacin da daya daga cikin masu girkin gidan ya shiga dakin Dr Rabe Nasir kuma ya kwankwasa kofa amma bai amsa ba. Bayan ganin jini sai ya kira jama'a."
"Da wuri mai girkin ya sanar da dogarin kwamishanan wanda ya shiga ya ga an boye gawar mamacin cikin bayin dake dakinsa."
Marigayin ya yi karatunsa a Jami'ar Abuja, Jami'ar Kansa Lawrensu da Jami'ar Bayero dake Kano.
Gabanin shiga siyasa, ya yi aiki da hukumar DSS da EFCC.
Gwamna Masari ya dira gidan kwamishinan da aka kashe, jami'ai sun cafke mutum daya
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, yana gidan kwamishinan da yan bindiga suka hallaka.
Kwamishinan yan sanda, Sanusi Baba, da shugaban jami'an tsaron farin kaya (DSS) reshen jaihar Katsina duk sun je gidan yayin da jami'an suka cigaba da kokarin ɓalle kofa domin ciro gawar.
Hakanan kuma jami'an sun gano wayar salula ta marigayi kwamishina da kuma ta wani mutum ɗaya daban.
Asali: Legit.ng