Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Masallaci a Neja, Sun Kashe 15 Sun Raunata Da Dama

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Masallaci a Neja, Sun Kashe 15 Sun Raunata Da Dama

  • Miyagun 'yan bindiga sun kutsa masallaci sun harbe a kalla mutane 15 har lahira a kauyen Ba'are a jihar Neja
  • Majiyoyi daga garin sun tabbatar da harin inda suka ce wadanda suka jikkata suna nan a babban asibitin Kontagora ana musu magani
  • Rundunar yan sandan jihar Neja ta bakin Kwamishina Bala Kuryas ta tabbatar da harin amma ta ce mutum 9 ne aka kashe

Neja - A kalla masallata 15 ne suka mutu yayin da wasu da dama suka samu rauni a harin da aka kai a masallaci da ke kauyen Ba'are a karamar hukumar Mashegu na jihar Neja.

Maharan sun kai harin ne yayin da mutanen kauyen ke sallar asubahi kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Masallaci a Neja, Sun Kashe 15 Sun Raunata Da Dama
Yan bindiga sun kai hari masallaci a Niger, sun bindige mutm 15. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Katsina ta bude layukan sadarwa a kananan hukumomi 17 na jihar

Wata majiya ta ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Kontagora domin yi musu magani.

Rundunar 'Yan sana ta tabbatar da harin

Kwamishinan yan sandan jihar Neja, Monday Bala Kuryas, ya tabbatar da harin, ya ce a kalla mutane 9 aka kashe a harin.

Ya ce:

"Tuni Rundunar 'yan sandan jihar Neja ta tura jami'an tsaro zuwa wuraren da abin ya shafa domin su tsare rayuka da dukiyoyin mutanen garin."

Ya jadada cewa hukumomin tsaro za su cigaba da yin ayyukansu na kiyaye rayuka da dukiyoyin yan jihar Neja da 'yan Najeriya yayin da ya ke kira ga al'umma su rika taimaka musu da bayanai masu amfani.

Wannan harin na zuwa ne kimanin watanni biyu bayan 'yan bindiga sun halaka mutane 18 a wani masallaci a karamar hukumar ta Mashegu.

An kai wancan harin ne a kauyen Mazakuka da ke karamar hukumar Mashegu a ranar 26 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Mafarauta sun kame 'yan bindiga 3 bayan doguwar musayar wuta

Sokoto: 'Yan ta'adda sun naɗa sabbin hakimai da dagatai, sun bude kasuwanni da gwamnati ta rufe

A wani labarin, yan ta'adda da aka fi sani da yan bindiga sun nada wasu mambobinsu a matsayin dagatai a wasu kauyuka a karamar hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.

A cewar wata jaridar intanet ta Sokoto, Daily Star, kasurgumin shugaban yan bindiga, Turji ne ya nada sabbin dagatan.

Rahoton ya ce an fara kiran yan ta'addan su kira yan kauyen Gangara su hallarci taro a kauyen Suturu a ranar Alhamis inda aka sanar da sauke tsaffin dagatan sannan suka nada mambobinsu a matsayin sabbin shugabanni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164