CBN ya ba bankin Sterling damar aiki a matsayin bankin Muslunci a Najeriya

CBN ya ba bankin Sterling damar aiki a matsayin bankin Muslunci a Najeriya

  • Hukumomin bankin Sterling na daf da zama kamfani mai rike da madafun iko bayan samun izini daga CBN
  • A matsayinsa na kamfani, bankin zai bude wani sabon reshen da zai yi aiki a matsayin bankin Muslunci
  • A cikin 'yan watannin da suka gabata, bankin First Bank da na Guaranty Trust duk sun sake fasalinsu zuwa kamfanoni

Babban bankin Najeriya (CBN) ya bukaci bankin Sterling Plc da ya ci gaba da aiwatar da shirinsa na gyarawa tare da gudanar da lasisinsa domin kirkirar tsarin mu'amala ba kudin ruwa.

Amincewar bisa ka'ida ce kuma karkashin amincewar tsarin CBN.

Sabon reshen na bankin Sterling da za a kira shi da Alternative Bank Limited zai kuma yi aiki a karkashin ka'idodin addinin Musulunci.

Bankin Sterling a Najeriya
CBN ya ba bankin Sterling damar aiki a matsayin bankin Muslunci a Najeriya | Hoto: businessday.ng
Asali: Twitter

Bankunan da ba na ruwa ba, wadanda aka fi sani da bankunan Muslunci sun dogara ne akan ma'anar ka'idoji addinin Musulunci kamar haramcin riba a rance da mu'amala.

Kara karanta wannan

An gurfanar da mutumin da aka kama da ATM 2,863 a Legas

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka kuma tsarin ya haramta mu'amala da sana’o’in da ba su dace ba kamar barasa, taba, kera alburusai da sauransu.

Tare da amincewar, sabon reshen bankin Sterling ya shiga jerin su Jaiz Bank, Taj Bank da kuma Lotus Bank Ltd wadanda a halin yanzu bankuna ne da ba ruwa a kasar.

A cewar Sterling, kamar yadda sauran bankunan Musulunci suke, Alternative Bank Ltd zai tabbatar da bin ka'idojin addini.

Bankin ya sanarwa Nigerian Exoffenceschange Ltd cewa sabon reshen yana daidai da izinin babban bankin na sake fasalin kamfani (HoldCo).

Sanarwar ta ce:

"Babban Bankin Najeriya (CBN) ya amince da Sterling Bank Plc a ka'idance na lasisin tsayawa kan ayyukansa na banki wanda ba mu'amala da kudin ruwa - da aka tsara ya zama Alternative Bank Limited."
"Amincewar ta biyo bayan amincewa-cikin ka'idar da aka bai wa bankin don sake fasalin kamfani (HoldCo) kuma yana karkashin cika sharuddan da CBN ta gindaya."

Kara karanta wannan

Yadda dukiyar Dangote ta kara yawa a 2021 fiye da ninkin yadda ya mallaka a baya

Bankin Sterling ya kuma bayyana cewa, sabon reshen nasa zai mayar da hankali ne kan gina kawancen da zai hada daidaikun mutane da ‘yan kasuwa da ke amfani da fasahar kere-kere don samar da ingantacen kasuwanci tare da magance bukatun kudi na yau da kullum.

Yadda dukiyar Dangote ta kara yawa a 2021 fiye da ninkin yadda ya mallaka a baya

A wani labarin, attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Aliko Dangote, yana kan ganiyar sake lashe wannan mataki a shekarar, matsayin da ya lashe tun a shekarar 2014 wanda kuma zai zarce a karo na biyu a jere a sashinsa na siminti.

Tashin farashin hannun jarin kamfanin simintin Dangote da na man fetur da taki sun taimaka wajen bunkasa arzikinsa da ya kai dala biliyan 2.3 a bana zuwa dala biliyan 20.1 a ranar 3 ga watan Disamba, wanda ya kasance mafi arziki tun 2014, inji Bloomberg Bilionaires Index.

Kara karanta wannan

Bayanan kudin Abacha da wadanda EFCC ta kwato sun yi batan dabo a CBN

A cewar Bloomberg, tsananin bukatar siminti da hauhawar farashin kayayyakin gine-gine a Najeriya, sun taimaka wajen habaka kudaden shiga na kamfanin Simintin Dangote.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.