Tsaro: Ko tausayi ba ka bani, kai kace sai kayi Shugabancin kasa: Akande ya fadawa Buhari a gabansa
- Shugaban jam'iyyar APC na farko ya bayyanawa Buhari cewa zaman lafiya yan Najeriya ke so
- Akande yace kowa na zagin Buhari kuma ana daura masa laifi saboda shine Shugaba
- Gwamnoni, Sanatoci, Sarakunan gargajiya da manyan yan siyasa sun halarci taron
Tsohon Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress, APC, Cif Bisi Akande, ya bayyanawa Shugaba Muhammadu Buhari dalilin da yasa bai tausayinsa bisa caccakarsa da yan Najeriya ke yi kan rashin tsaro.
Tun bayan hawan Shugaba Buhari kan karagar mulki a 2015, matsalar tsaro a Najeriya ya tashi da yaki da Boko Haram zuwa rikicin makiyaya da manoma, yanzu kuma garkuwa da mutane.
Bisi Akande a gaban Shugaba Buhari yau a Legas ya bayyana masa shi ya nemi zama shugaban kasa saboda haka ya magance matsalar.
Akande ya yi jawabi ne yayin bikin kaddamar da littafin rayuwarsa dake gudana yau Alhamis, 9 ga Disamba a Eko Hotel and Suites, Victoria Island, Lagos, rahoton Vanguard.
Akande yace:
"Mun san kana son kasar, amma muna son zaman lafiya a kasar nan, kuma muna son cigaba. Muna zaginka kan komai da ke faruwa da kasar."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Mun san mu macuta ne, kuma laifinmu ne amma muna daura maka. Bana tausayinka saboda kai ka nemi aiki."
Manyan mutanen da suka halarta
Wadanda ke hallare a taron sun hada da Jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu; Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola; da Kakakin majalisar Legas, Mudashiru Obasa.
Hakazalika akwai tsohon Gwamnan Ogun, Gbenga Daniel; Gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrasak; Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni; Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun.
Oban Ife, Oba Enitan Ogunwusi, da Sarkin Lagos, Rilwan Akiolu.
Sauran sune shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, Sanata Tokunbo Abiru, Sanata Solomon Adeola, Opeyemi Bamidemi, Sanata Musuliu Obanikoro, Sanata Ganiyu Olarewanju Solomon, GOS, Sanata Tokunbo Afikuyomi, dss.
Asali: Legit.ng