An Bindige Jami'in FRSC Har Lahira A Kofar Gidan Abokinsa

An Bindige Jami'in FRSC Har Lahira A Kofar Gidan Abokinsa

  • ‘Yan bindiga sun harbe jami’in hukumar kiyaye haddura ta FRSC, Mr Omiwoye Sunday har lahira a jihar Ondo
  • Sun halaka marigayin ne a kofar gidan abokinsa, yayin da yake kokarin taka musu birki akan kai wa jama’a farmaki
  • Lamarin ya auku ne a daren Lahadi a wuraren Agbala kusa da Makarantar Saint Monica’s Girls Grammar cikin Ondo

Jihar Ondo - ‘Yan bindiga sun halaka wani jami’in hukumar kiyaye hadurra ta FRSC, Mr Omiwoye Sunday a cikin jihar, Daily Trust ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda su ka halaka jami’in a kofar gidan wani abokinsa yayin da yake kokarin hana su kai wa jama’a farmaki.

An Bindige Jami'in FRSC Har Lahira A Kofar Gidan Abokinsa
Bata gari sun bindige wani jami'in FRSC a Ondo. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Ba Kayan Matan Jaruma Ne Ya Raba Aure Na da Laila Ba, Baƙin Halinta Ne – Biloniya, Ned Nwoko

Lamarin mara dadin ji ya auku ne da daren Lahadi wuraren Agbala kusa da makarantar Saint Monica’s Girl Grammar a Ondo.

Ya je kai wa abokinsa ziyara ne lamarin ya auku

Daily Trust ta ruwaito yadda ganau su ka ce ya je gidan abokinsa tare da matarsa ne, inda ya tsayar da babur din shi a kofar gidan.

Anan ne wasu mutane su ka karasa kusa da don neman taimako daga dukansu da mutanen su ke yi.

Ya yi kokarin dakatar da ‘yan bindigan wadanda su ka yi gaggawar dauke shi da bindiga wanda take a wurin ya fadi matacce.

A cewar matarsa, Mrs Bunmi Sunday, ita da mijinta sun kai wa wani abokinsa wanda yake kusa da unguwarsu ziyara ne.

Har da wayarsa da babur dinsa su ka tsere

Kamar yadda ta ce:

“Take anan wasu suka gudo kusa da inda muke tsaye. Mijina ya yi kokarin tsayar da babur dinsa. Daga nan ‘yan bindigan su ka matso kusa da babur dinshi su na dukan matasan da suka gudo kusa da mu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta

“Mijina ya yi kokarin dakatar da su. Sun shaida masa cewa ba ta shi suke yi ba, a lokacin na yi sauri na shiga gidan amma mijina ya ki sauraronsu ya tsaya gefen babur dinshi. Daga baya muka ji harbi wanda mu na dubawa mu ka ganshi cikin jini, har sun harbe shi sun tsere da wayarsa da babur dinshi.”

Abokan aikinsa sun ce mutumin kirki ne shi

Abokan aikin mutumin sun kwatanta shi a matsayin mutumin kirki, tuni aka wuce da gawarsa asibitin kwararu da ke Ondo.

Wasu mazauna yankin sun bayyana yadda ake yawan kai farmaki wurin cikin kwanakinnan.

Daily Trust ta bukaci jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Funmilayo Odunlami, amma hakan bai yuwu ba har aka kammala rubuta rahoto.

Buhari ga jami'an tsaro: Bana son sake jin motsin ƴan bindigan hanyar Kaduna zuwa Abuja

A wani labarin, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci shugabannin tsaron kasar nan da su kawo karshen ta’addancin da ke aukuwa a kasa musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun bindige wani malamin kwaleji a jihar Benue

Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a ranar Alhamis bayan wani taro da shugaban kasa ya yi da kwamitin tsaron kasa, NSC a fadarsa da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa shugaban kasan ya ba ‘yan sanda da duk wasu jami’an tsaro ciki har da jami’an binciken sirri umarnin kada su zauna har sai sun kawo karshen ta’addanci, rashin tsaro, amsar kudaden fansa da sauransu a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: