Babbar magana: 'Yan sanda sun shiga damuwa bayan jin shuru na albashin Nuwamba
- 'Yan sandan Najeriya sun shiga damuwa yayin da ma'aikatar kudi ta jinkirta biyansu albashin watan Nuwamba
- A halin yanzu dai 'yan sanda basu samu albashi ba, wanda suka saba karba a ranakun 25 ga kowace wata
- An ba jami'an rundunar hakuri, inda aka bayyana musu dalilai da suka jawo har aka jinkirta albashin watan
Najeriya - Jami’an ‘yan sandan Najeriya har yanzu ba su samu albashin watan Nuwamba ba, sakamakon zargi kan wasu ma’aikatan ma’aikatar kudi, kasafin kudi da tsare-tsare ta kasa suka yi na gudanar da biyan kudaden.
Dangane da wannan al’amari, hukumar ‘yan sanda ta kai dauki domin kwantar da tarzoma daga wanda ke korafin rashin biyansu albashi mako guda kenan a watan Disamba.
Punch ta tattaro cewa ‘yan sanda yawanci suna karbar albashi ne a ranar 25 ga kowane wata amma abin da ya faru a yanzu na kara haifar da damuwa a cikin ‘yan sandan.
Ba a dai iya tabbatar da ko akwai wasu dalilan da suka haddasa tsaikon ba amma Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya Usman Baba ya umurci mataimakin sufeto-Janar na ‘yan sanda da kwamishinonin ‘yan sanda na shiyyoyi da su lallabi mutanen su.
A cikin wani sako a ranar 3 ga Disamba, 2021, wanda aka tura ga AIGs da CPs da ke kula da rundunoni daban-daban, IG ya bayyana dalilin jinkirin tare da ba su tabbacin cewa ana kokarin ganin an biya su cikin gaggawa.
A cewar SaharaReporters, Sakon mai lamba CV:3940/PB/FHQ/ABJ/VOL45/8 DTO: 031350/12/2021 da taken, ‘Shirin albashi,’ ya karanta:
“Bayanin da aka samu daga sashin IPPIS (Integrated Payroll and Personnel Information System) na OAGF (Ofishin Babban Lauyan Tarayya) na nuna jinkirin da ake samu wajen sarrafa kudade daga Ma’aikatar Kudi ta Tarayya don biyan albashin watan Nuwamba 2021 wanda ke nuna cewa akwai yiwuwar jinkirta biyan albashin Nuwamba 2021.
“Duk da haka, INGENPOL (Sufeto-Janar na ‘yan sanda) ya yaba da sadaukarwa da sadaukarwar jajircewar jami’an rundunar. Don haka ya ke yin mai yuwuwa domin ganin an rage jinkirin."
Sai dai ‘yan sandan da suka nemi a sakaya sunansu sun ce yanzu ma ana shan fama a rayuwar yau da kullum, suna mamakin dalilin da ya sa aka yi jinkirin biyansu dan karamin albashin su.
Wani dan sanda da ke aikin gadi a wani kamfani a rukunin masana’antu na Idu, Mbora da ke Abuja, ya ce yana shan wahalar zuwa wurin aiki saboda ba shi da kudin zirga-zirga.
Ya koka da cewa:
“Ba zan zo aiki ba idan da a hedkwatar rundunar nake aiki saboda ba ni da kudin zirga-zirga. Na kasance ina karbar kudi don in zo aiki; abubuwa suna bani wahala a yanzu."
Sai dai kakakin rundunar, Frank Mba, ya ce ‘yan sandan sun samu tabbacin za a biya su a ranar Juma’a.
Ya ce:
“Mun samu tabbacin za a biya su ranar Juma’a kuma ba wai kawai na ‘yan sanda ba ne. Albashin ‘yan sanda, tabbas, kun san gwamnatin tarayya ce ke biya kuma albashin ma’aikatan tarayya yakan fito ne ta IPPIS.
"Muna sane da cewa akwai sauran MDA sama da 20 da ke fuskantar irin kalubalen da 'yan sanda ke fuskanta amma gwamnati ta ba mu tabbacin cewa za a magance kalubalen mu kuma da fatan nan da kwanaki biyu masu zuwa hakan zai kare."
'Yan sanda sun runtuma kame a Abuja, sun harbi jami'in DSS
A wani labarin, jami’an ‘yan sanda daga sashin Zuba da ke babban birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a, sun runtuma kame a unguwar Dakwa da ke Abuja, inda suka harbe wani jami’in hukumar DSS.
Jami’in na DSS da ba a gano waye shi ba an ce yana kan hanyar wucewa ne a lokacin da aka harbe shi a kamen na Dakwa, Daily Trust ta ruwaito.
Akalla mutane 37 ne da wasu masu wucewa ta yankin aka kama a yayin samamen da aka gudanar da misalin karfe 8 na dare.
Asali: Legit.ng