Dalilin da yasa muka haramta shan Shisha a jihar Kano, Yusuf Ibrahim Lajawa
- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana dalilin da yasa ta haramta shan tabar Shisha a fadin jihar
- Gwamnatin tace za ta kafa hukumar garkame wadanda aka kama masu karya dokar kuma ta ci su tara
- An dau wannan mataki ne don rage alfasha da abubuwan da ka iya gurbata tarbiyyan yara
Shugaban hukumar yawon bude ido na Kano, Yusuf Ibrahim Lajawa, ya ce ta'amuni da muggan kwayoyi da shaye-shaye yasa Gwamnatin jihar ta haramta shan tabar Shisha a fadin jihar.
Lajawa ya bayyana hakan yayin hira da Kano/Jigawa Chronicle.
A cewarsa, sun dau matakin ne saboda sun gano yawancin masu Shan tabar Shisha suna fita daga hayyacinsu.
Lajawa yace:
"Bayan binciken da Likitocinmu suka gudanar, an samu cewa ana amfani da Shisha wajen fara ta'amuni da muggan kwayoyi."
"An kafa dokar a 1994 amma daga baya akayi mata gyaran fuska kuma Gwamna ya rattafa hannu a Nuwamban 2021."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Ana shirya matakan dabbaka wannan doka ta hanyar kafa hukumar garkame wadanda aka kama masu karyata da kuma cin su tara ko kuma kulle shagunan shan Shisha a jihar."
Ya kara da cewa sun dau wannan mataki ne don rage alfasha da abubuwan da ka iya lalata tarbiyya.
Gwamnati ta amince da bude gidajen shan Shisha a kasar Saudiyya
A wani labarin kuwa, an amince a sha shisha a wuraren shan gahawa a Saudiyya daga ranar Litinin yayin da ake sassauta dokar kullen korona a ƙasar, rahoton Saudi Gazzete.
Bayan shekara guda, Saudiyya ta fara sassauta dokokin kulle sakamakon annobar cutar Korona.
Cikin sharrudan da ma’aikatar kula da birane da karkara ta gindaya domin amincewa mutum ya shiga shagon Shisha shine ya kasance ya yi rigakafin Korona.
Hakazalika wajibi ne dukkan ma'aikatan shagunan su rika yin gwajin korona mako-mako.
Asali: Legit.ng