Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya sabon jarabawa wa Malaman makaranta 35,000

Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya sabon jarabawa wa Malaman makaranta 35,000

  • Gwamnatin Malam Nasir El-Rufa'i ta fara gwada Malaman makarantu 35,000 don tabbatar da kwarewarsu
  • Shekaru hudu hudu kenan bayan sallamar Malamai sama da 20,000 da suka fadi jarabawar a baya
  • Kungiyoyin kwadago da na Malamai sun yi kira ga mambobinsu kada su zana jarabawar

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da wani sabon jarabawan da aka shiryawa Malaman Firamare a jihar don tabbatar da kwarewarsu wajen koyarwa.

Wannan na zuwa ne shekaru hudu yanzu bayan gudanar da irin wannan jarabawa kuma mutum 22,000 suka fadi.

Shugaban hukumar kananan makarantu, Tijjani Abdullahi, ya bayyana cewa manufar zana wannan jarabawa ba don a kori mutane bane, amma kawai so ake a kawo gyara don sake horar da Malamai, rahoton ChannelsTV.

Kara karanta wannan

Ba zan sake Zina ba sai Allah ya bani miji, Jarumar Nollywood

Ya bayyanawa manema labarai cewa yanzu an canza tsarin daga rubutu a takarda zuwa yi a Komfuta, yace:

"Malaman dake nan zasu ga canjin da akayi wajen tsarin jarabawan."

A jawabin da Gwamnan jihar, Nasir El-Rufa'i, ya daura a shafinsa na Facebook ya bayyana cewa Gwamnatin ta yi watsi da barazanar kungiyar kwadagon Najeriya da kungiyar Malaman Makaranta.

Malaman zasu yi gwaji ne a madodi irinsu Lissafi, Yaren Turanci, ilmin zamantakewa, da Kimiya.

Malaman makaranta 35,000
Gwamnatin jihar Kaduna ta shirya sabon jarabawa wa Malaman makaranta 35,000 Hoto: Governor of Kaduna State
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng