Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota ranar Talata

  • A jiya Talata ne aka samu faruwar wani hadarin mota a wani yankin jihar Legas, lamarin da ya jawo tada hankulan matasa
  • An ruwaito cewa, wata babbar mota ce ta samu matsalar birki ta kuma take mutane da yawa a yankin
  • 'Yan sanda sun bayyana adadin mutanen da suka mutu, tare da shaida adadin wadanda suka ji munanan raunuka

Jihar Legas - Rundunar ‘yan sandan Legas ta ce dalibai biyu ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya afku a kan hanyar Ogunnusi, TheCable ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata wanda ya kai ga mazauna yankin suka rufe wani bangare na titin da tayoyi domin nuna adawa da hadarin.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin ranar Talata, Adekunle Ajisebutu, kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar Legas, ya ce wasu mutane 12 sun samu raunuka a hadarin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta

Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu
Rahoton ‘yan sanda: Dalibai biyu sun mutu, 12 sun jikkata a hatsarin babbar mota a Legas | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ajisebutu ya ce a halin yanzu wadanda suka jikkata na samun kulawar likitoci.

Sanarwar ta 'yan sanda ta bayyna cewa, lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:15 na yamma, inda babbar motar kirar DAF da wani Bolaji Kabiru ke ja ta samu matsalar birki.

Hakazalika, sanarwar ta ce maza biyu sun mutu nan take, yayin da wasu mata bakwai da maza biyar suka jikkata.

Ta kara da cewa:

“Jami’an da ke kula da zirga-zirgar ababen hawa na sashen ‘yan sanda na Ojodu sun ziyarci wurin.
“An kwashe gawarwakin daliban da suka mutu (har yanzu ba a san ko su waye ba) tare da goyon bayan jami’an FRSC kuma an ajiye su a dakin ajiye gawa na babban asibitin Mainland, Yaba, domin a tantance su.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Garin rage mata hanya, an sace yarinya mai shekaru 5 a jihar Kano

"An kai wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Apple City, Ojodu Berger; Asibitin St. Michael, Ojodu; da Asibitin Taimakon Gaggawa na Jihar Legas, Toll Gate."

A bangaren matasa a wurin, matasa sun fusata, inda suka bayyana bukatar a mika musu direban motar, lamarin da ya kai ga lalata motoci hudu bayan kin mika direban, Punch ta ruwaito.

Domin kwantar da tarzomar, gwamnatin jihar Legas ta turo jami'an 'yan sanda domin kiyaye faruwar rikici a yankin.

Zuwa yanzu dai an ajiye direban a ofishin 'yan sanda, inda aka bukaci mazauna su kwantar da hankula su zauna lafiya.

Birkin babbar mota ya balle, ta murkushe kananan yara 'yan makaranta

A baya mun kawo muku cewa, akalla yara ‘yan makaranta 13 ne suka mutu a Legas a ranar Talata bayan da wata motar dakon kaya ta samu matsalar birki ta bi ta kansu, kamar yadda shaidu suka bayyana.

Yaran suna dawowa daga makaranta ne lokacin da lamarin ya faru, Premium Times ta ruwaito. Kawo yanzu dai ba a tantance adadin wadanda suka mutu ba.

Kara karanta wannan

Jihar Niger: 'Yan bindiga na karbar sigari da wiwi a matsayin kudin fansa

Hadarin ya afku ne a kan titin Isheri, daf da ofishin ‘yan sanda na Ojodu yayin da yaran suka taso daga makaranta, inji rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.