Rikci ya kaure kan bayar da kwangilar N42bn ta gyaran majalisar tarayya

Rikci ya kaure kan bayar da kwangilar N42bn ta gyaran majalisar tarayya

  • Batun ware naira biliyan 42 don gyaran majalisar tarayya ya janyo cece-kuce daga ‘yan majalisar da kuma masu ruwa da tsaki
  • Musamman idan aka duba cewa aikin zai yuwu da naira biliyan 26.9 kamar yadda asalin kamfanin da ya gina majalisar ya kiyasta
  • Bincike ya nuna yadda ‘yan majalisa da dama suka dinga nuna rashin amincewarsu akan kwangilar wacce kamfanin Messrs Visible Construction Limited zai yi

Abuja - Batun yunkurin gyaran majalisar tarayya da naira na gugar naira biliyan 42 ya janyo cece-kuce musamman daga ‘yan majalisar da kuma masu ruwa da tsaki.

Musamman idan mutum ya kalli yadda za a iya amfani da naira biliyan 15 ko kuma kasa da hakan wurin aiwatar da gyaran bayan asalin maginan wurin sun kiyasta naira biliyan 26.9 a matsayin kudin da zai isa, amma duk don a duba wa kamfanin kwangilar wanda har yanzu ba a samu wani bayani na wata kwangila da ya taba aiwatarwa ba aka ba shi aikin.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya yiwa sojojin da suka raunata a yaki da ISWAP abin alheri na kudade

Rikici ya barke kan kwangilar N42bn na gyaran zauren majalisar tarayya
Rikici ya barke kan kwangilar N42bn na gyaran zauren majalisar tarayya. Hoto daga leadership.ng
Asali: Facebook

Binciken Leadership ya bayyana yadda wasu ‘yan majalisa da dama suka nuna rashin amincewarsu da kwangilar da kuma irin dukiyar da aka ware don kwangilar, har da kuma rashin tabbaci akan kamfanin Messrs Visible Construction Limited, wanda aka ba damar aiwatar da kwangilar.

FCDA ta bayar da kwangilar gina majalisar tarayya ga ITB Nigeria a ranar 18 ga watan Fabrairun shekarar 1996 lokacin mulkin soji na Janar Sani Abacha da dala miliyan 35.18.

An kammala bangaren ta na farko a shekarar 1990 da doriya, an yi dayan bangaren tsakanin 2007 da 1999.

Fiye da shekaru 20, ba a sake gyara majalisar ba. A 2019 da aka yi sabbin shugabannin majalisar, shugaban majalisa Ahmed Lawan da kakakinta, Femi Gbajabiamila, bayan sun shiga ofishinsu suka nufi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da batun gyaran majalisar.

Kara karanta wannan

Dangote ya fi kasashe 30 na Afrika arziki bayan tashin farashin simintin kamfaninsa

An kiyasta naira biliyan 37 zai isa gyaran inda koken da ‘yan Najeriya da dama suka dinga yi ya janyo aka dakatar da aikin.

Annobar Coronavirus a 2020 ta ja an zare naira biliyan 9 daga cikin kudaden ba tare da an mayar ba.

Yayin tattaunawa akan batun da shugaba kwamitin ayyuka na majalisar, Sanata Sani Musa, ya ce ‘yan majalisa suna ta magana akan gyaran amma mutanen da ba su san rubuwar da ginin ya yi ba suna ta kokarin hana gyaran.

Kakakin majalisar, Ajibola Basiru, ya ce har yanzu ba su amshi ko sisi ba a cikin naira biliyan 37 din gyaran majalisar da ake ta cece-kuce akai, duk da yadda a ranar 21 ga watan Yunin 2021 saman kwanon majalisar ya ruguza har ruwa ya dinga zuba.

Kudin da aka gabatar na gyaran shi ne N42,412,917,272, kenan an samu karin naira miliyan 5 akan asalin kudin da aka amince da su na naira biliyan 37.

Kara karanta wannan

Ayyuka 257 aka kwafo daga kasafin kudin 2021 masu darajar N20bn, ICPC

Wadanda suka tayar da hankali akan gyaran sun duba ne inda suke tambayar dalilin da zai sa a kara naira biliyan 5 akan asalin kudin.

Wani dan majalisa wanda ya so a boye sunansa yayin tattaunawa da Leadership ya yi mamakin dalilin ba Messrs Visible Construction Limited kwangilar aikin.

Majiyar ta ce ITB Nigeria Limited ta ce naira biliyan 26.9 zai isa a yi gyaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng