'Yan sanda na kama makiyaya da basu da laifi, suna alakanta su da satar mutane, Miyetti Allah

'Yan sanda na kama makiyaya da basu da laifi, suna alakanta su da satar mutane, Miyetti Allah

  • Kungiyar makiyaya ta Najeriya ta Miyetti Allah Kautal Hore, ta zargi 'yan sanda da tatsar Fulani da ke kauyukan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja
  • Sakataren kungiyar na kasa, Saleh Alhassan, ya ce 'yan sanda suna kama makiyaya da ke kiwonsu inda suke musu sharri da garkuwa da mutane ko fashi
  • A cewar Alhassan, su na karbar kudin beli da ya ke kai N200,000 zuwa N1.5 miliyan daga makiyayan da suka mannawa sharrin

Daya daga cikin kungiyoyin makiyaya ta Najeriya, Miyetti Allah Kautal Hore, ta zargi 'yan sanda da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da kama Fulani makiyaya da basu da laifi, sannan su manna musu sharrin garkuwa da mutane kuma su sanya su biyan makuden kudin beli.

Kara karanta wannan

Buhari ya tabbatarwa 'yan Najeriya zaman makoki a kasar na daf da zuwa karshe

Punch ta ruwaito cewa, sakataren kungiyar na kasa, Saleh Alhassan, ya sanar da wannan zargin ne a wata takarda da ya fitar ranar Juma'a.

'Yan sanda na kama makiyaya da basu da laifi, suna alakanta su da satar mutane, Miyetti Allah
'Yan sanda na kama makiyaya da basu da laifi, suna alakanta su da satar mutane, Miyetti Allah. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Kamar yadda yace, Fulani marasa laifi da ke kiwo a kauyukan da ke kusa da babbar hanyar ne 'yan sanda ke kamawa a cikin kwanakin nan kuma dole ta sa suke biyan makuden kudade.

Mai magana da yawunsu ya ce, a kundun tsarin mulki, beli kyauta ne "amma 'yan sandan da ke ofishin Katari a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna, beli ya fi komai tsada".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ana tirsasa wadanda ake zargi wurin biyan kudi mai yawa domin a sake su ko kuma a azabtar da su. 'Yan sandan na zuwa su sace makiyaya, su dinga kiransu da masu garkuwa da mutane ko kuma 'yan fashi, ta hakan ne suke samu su karba kudi ko su azabtar da su.

Kara karanta wannan

Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko

“Makiyayanmu da ke ayyukansu, su ke shan wahala wadannan 'yan sandan kuma su bukaci beli. Da yawa daga cikin 'yan uwan makiyayan nan suna biyan daga N200,000 zuwa 1.5 miliyan na beli.
"A gaskiya ba za mu lamunci hakan ba kuma muna bukatar a dauka matakin gaggawa.
"A yayin da muka sanar da hedkwatar 'yan sanda abinda ke faruwa, mun ga ya dace mu sanar da duniya ganin irin wannan kiyayya da rashin adalci da ake yi wa makiyaya da Fulani a kasar nan," takardar tace.

Alhassan ya yi kira ga hukumar 'yan sandan Najeriya da su bibiya tare da damke jami'an da ke da hannu a cikin lamarin, Punch ta ruwaito.

Kakakin rundunar 'yan sandan Najerya, Frank Mba, bai yi martani kan sakon kar ta kwana da aka tura masa ba kafin rubuta wannan rahoton.

'Yan sanda sun yi ram da dan fashin da yayi basaja kamar makiyayi

Kara karanta wannan

2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai

A wani labari na daban, wani mutum da ake zargi da fashi da makami mai suna Biodun Rasheed, wanda yayi shiga tamkar makiyayi ya shiga hannun rundunar 'yan sandan jihar Ogun.

Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Ogun sun yi ram da wanda ake zargin yayin da ya ke tsaka da fashi da makami, Daily Trust ta ruwaito hakan.

'Yan sandan da ke aiki da ofishin Kemta a karamar hukumar Odeda ta jihar sun samu kiran gaggawa kan cewa 'yan fashi da makami na barna a mile 6 da ke kan titin Ajebo a garin Abeokuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng