Abdullahi Abbas, Sule Garo da wasu yan siyasa 5 suka dau nauyin kaiwa ofishinmu hari: Shekarau
- Rikicin jam'iyyar APC a Kano tsakanin bangaren Gwamna da Sanata Shekarau ya ki ci, ya ki cinyewa
- An kai karan wasu mabiya Gwamna Ganduje ofishin Sifeto Janar na yan sanda kan laifin kaiwa yan sashen Shekarau hari
- Wasu bata gari sun kai hari ofishin yakin neman zaben Sanata Barau Jibrin ranar Alhamis inda suka banka wuta
FCT, Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau; Sanata Barau Jibrin da wasu mambobin majalisar wakilan tarayya sun kai kai wajen Sifeto Janar na yan sanda, IGP Baba Alkali.
Yan majalisan sun shigar da kara hedkwatar yan sanda ne bisa harin da aka kai ofishin yakin neman zaben Sanata Barau Jibrin ranar Alhamis, 2 ga Disamba.
Wadanda suka rattafa hannu kan takardar sun hada da Senator Shekarau (Kano ta tsakiya), Senator Barau (Kano ta kudu), ;Nasiru Abdua, Tijjani Abdulkadir Jobe, Shaaban Sharada, da Haruna Isa Dederi.
Yan majalisan sun ce an kai harin ne sakamakon nasarar da suka samu a kotu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A karar da suka shigar, sun ce Shugaban jam'iyyar na bangaren gwamna, Alhaji Abdullahi Abbas da kwamishanan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, suka dau nauyin hare-haren.
Sauran wadanda sukayi zargi sune shugaban karamar hukumar Kano Municipal, Faizu Alfindiki; Shugaban karamar hukumar Gwale, Khalid Ishaq Diso; Shugaban karamar hukumar Kumbotso, Hassan Garban Kauye; da Shugaban karamar hukumar Nasarawa, Auwal Lawan Shuaibu.
Wani sashen karar yace:
"Zaku tuna cewa ranar 30 ga Nuwamba, babbar kotun Birnin tarayya ta yanke hukunci kan lamarin zaben shugabannin APC a Kano kuma wadanda suka sha kasa basu ji dadi."
"Maimakon su yi yakinsu a kotu, sun koma kai hare-hare."
"Sun yi kokarin kona ofishin jam'iyyarmu dake Zaria Road don kashe mazauna da ji musu rauni."
Sanata Shekarau da sauran yan majalisan sun ce duk abinda ya faru da su a kama wadannan da suke zargi.
Siyasar Kano: Yan sanda sun damke mutum 13 da hannu a ƙone ofishin jam'iyyar APC na tsagin Shekarau
Hukumar yan sanda reahen jihar Kano, ranar Alhamis, tace ta damke mutum 13 dake da hannu a kone ofishin yakin neman zaɓen gwamna na Sanata Barau Jibrin.
Tribune Online ta rahoto cewa wasu yan daba sun kona ofishin, wanda ke a kan hanyar Maiduguri a cikin birnin Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa yan daban suna ɗauke da makamai masu hatsari, wanda ya tilasta wa mutanen yankin nesa da su kada abin ya shafe su.
Asali: Legit.ng