An tura dakarun Sojoji Najeriya kasar Mali don tabbatar da zaman lafiya

An tura dakarun Sojoji Najeriya kasar Mali don tabbatar da zaman lafiya

  • Hukumar Sojojin Najeriya ta tura wasu dakarunta kasar Mali don samar da zaman lafiya ga al'ummar
  • Jami'an Sojoji sama da sittin da aka tura sun kwashe makonni suna horo na musamman
  • Rikicin Shugabancin a Mali ya haifar da rashin zaman lafiya kuma majalisar dinkin duniya ta sanya baki

Kaduna - An tura dakarun Sojojin Najeriya 62 dake cibiyar samar da zaman lafiya don tunawa da Martin Luther Agwai (MLAILPKC) kasar Mali don aikin samar da zaman lafiya.

An tura jami'an ne bayan makonni uku ana musu horo bisa ka'idojin majalisar dinkin duniya, Kwamanda ciar (MLAILPKC), Manjo Janar Auwal Fagge ya bayyana.

Daily Trust ta rahoto cewa Manjo Janar Fagge ya bayyana hakan ne a taron yaye Sojojin bayan horo a Jaji, jihar Kaduna.

Yace:

"Sashe farko na horon ya hada da kwarewa wajen rike makamai, da salon aikin soja. Sashe na biyu na horon ya koyawa Sojojin yadda ake samar da zaman lafiya bisa sharrudan majalisar dinkin duniya."

Kara karanta wannan

Borno: Mayakan ISWAP sun kashe babban kwamandan sojoji a Rann

"Hakazalika ya hada da darrusan yadda ake kare farar hula, yadda ake kare mata daga fyade da yara."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tura dakarun Sojoji Najeriya kasar Mali
An tura dakarun Sojoji Najeriya kasar Mali don tabbatar da zaman lafiya Hoto: NA
Asali: UGC

Shugaban horo na hedkwatar hukumar Sojin Najeriya, Manjo Janar AbdulSalam Ibrahim, wanda yayi babban bako a taron a bayyana cewa horon da aka yiwa dakarun zai taimaka musu matuka wajen gudanar da aikinsu a Mali.

Shugaban ya samu wakilcin Birgediya Janar Hassan T Dada.

Borno: Mayakan ISWAP sun kashe babban kwamandan sojoji a Rann

Ana zargin mayakan ISWAP sun halaka daya daga cikin kwamandojin bataliyoyi daga rundunar Operation Hadin Kai, kamar yadda wata majiya ta sanar da The Cable.

Ana zargin sun halaka babban sojan tare da wasu sojoji biyar bayan sun kai farmaki Rann, wani gari da ke karkashin karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotun daukaka kara ta sako faston da aka yanke wa hukuncin daurin rai da rai

An samu bayanai akan yadda musayar wuta ta auku tsakanin sojojin da mayakan na tsawon sa’o’i.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng