Labari cikin hotuna: Ganduje ya nada Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishinan ilimi 2

Labari cikin hotuna: Ganduje ya nada Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishinan ilimi 2

  • Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya nada Alaramma Malam Ahmad Sulaiman Ibrahim kwamishinan ilimi na 2 a jihar
  • Alaramman ya wallafa hotuna inda gwamnan ke mika masa takardar kama aiki inda suke tare da Sheikh Balalau da Sheikh Kabiru Gombe
  • Bayan mika godiyarsa ga Allah, ya bukaci jama'a da su taya shi da addu'a domin sauke nauyin wannan jarabta da Allah yayi musu

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya nada Sheikh Alaramma Malam Ahmad Sulaiman Ibrahim kwamishinan ilimi na biyu a jihar.

Kamar yadda Alaramman ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya mika godiya ga Allah madaukakin Sarki tare da mika godiya a madadinsa da iyalansa ga Gwamnan.

Labari cikin hotuna: Ganduje ya nada Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishinan ilimi 2
Labari cikin hotuna: Ganduje ya nada Alaramma Ahmad Sulaiman kwamishinan ilimi 2. Hoto daga Ahmad Sulaiman Ibrahim
Asali: Facebook

Kamar yadda wallafar tace:

"Godiya ta tabbata ga Allah. Dukkan godiya ta tabbata ga Allah madaukakin sarki. Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammadu S. A. W.

Kara karanta wannan

Sabbin hotunan El-Rufai inda ya ɗau wankan jins tamkar wani saurayi yayin da ya fita duba wasu ayyukan jiharsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bayan haka, a madadina da na iyalaina da al'ummar da ta ke tare da mu, muna mika godiya mai tarin yawa ga mai girma Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduja, Khadimul Islam, bisa nada ni da yayi a kwamishina na 2 a hukumar ilimi ta jihar Kano.
"Ina rokon Allah ta'ala ya sanya alheri, yasa mana albarka cikin wannan kujera da ya ba mu dan ya jarabce mu.
"Ina so in yi amfani da wannan dama wajen rokon 'yan uwa na duniya da su taya mu da addu'a don ba za mu iya ba, Allah ya iya mana.
"Daga karshe ina so in dan yi tsokaci ga 'yan uwa, ba komai za mu iya hanga wanda ya ke ta bangaren wannan kujera ba, idan an ga mun sauka a layi, to a yi kokari a tina mana domin mu gyara ba a je a yi ta surutu ba.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Kotu ta sake sakin jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a zaman shari’ar yau

"Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya a jihar mu da ma kasa baki daya, Nagode."

Kano Tumbin Giwa: Ganduje ya dauki masu rawar koroso 45 aikin dindindin

A wani labari na daban, a ranar Laraba da ta gabata, gwamnatin jihar Kano ta mika takardun daukar aikin dindindin ga masu rawar gargajiya wadanda aka fi sani da 'yan rawan koroso 45 a jihar.

Sabbin ma'aikatan rawan da aka dauka aiki an saka su a matsayin kananan ma'aikata ne wadanda za su yi aiki karkashin ma'aikatar tarihi da ofishin al'adu na jihar.

A yayin mika takardun daukar aikin a ma'aikatar, kwamishinan ma'aikatar al'adu, Ibrahim Ahmad Karaye, ya yi bayanin cewa wannan kyautatawar an yi ta ne domin karrama kananan ma'aikata masu aiki tukuru.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng