An gurfanar da wata mata a kotu kan satar katin waya na N1m
- An gurfanar da Oyinkansola Shosan a kotun majistare da ke Ikeja a jihar Legas ranar Alhamis bisa zarginta da sace katin waya mai kimar naira miliyan daya
- Sai dai Shosan ta musanta aikata wannan laifin inda alkali ya bukaci ta biya belin N500,000 tare da gabatar wa da kotu tsayayyu guda biyu
- Alkalin ya bukaci tsayayyun su kasance masu ayyukan yi kuma su nuna alamar biyan harajinsu na shekaru biyu ga gwamnatin jihar Legas
Legas - An gurfanar da Oyinkansola Shosan mai shekaru 37 gaban kotun majistare da ke zama a Ikeja ranar Alhamis bisa zarginta da satar katin waya mai kimar Naira miliyan 1, NewsWireNGR ta ruwaito.
Shosan wacce take zama a Abule-Egba a cikin jihar Legas ta gurfana gaban alkali Mrs O.A Darisu, bisa zarginta da sata.
Sai dai wacce ake zargin ta musanta laifin wanda daga nan kotu ta bukaci ta biya belin N500,000 tare da gabatar da tsayayyu biyu.
Tsayayyun su kasance su na ayyuka masu kyau
Alkalin ta ce tsayayyun su kasance su na yin ayyuka masu kyau kuma su gabatar da shaidar biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas na shekaru biyu.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dan sanda mai gabatar da kara, Sifeta Mojirade Edeme ya sanar da kotu cewa wacce ake zargin ta aikata laifin ne a ranar 15 ga watan Oktoba a Ikeja, jihar Legas.
NewsWireNGR ta bayyana yadda Edeme ya ce wacce ake zargin ta saci katin waya mai yawan gaske daga Bitis Telecommunication.
Kamar yadda ya shaida:
“Mai kara ya ba wacce yake karar katin iri daban-daban na N1,000,000 don ta siyar masa.
“Sai dai ya yi mamakin ganin yadda katin mai kimar da ya fada ya yi layar zana.
“Bayan tambayarta ne ta kasa bayar da wata gamsasshiyar amsa.”
Akwai yuwuwar ta kwashe shekaru 7 a gidan yari
Wacce ake zargin ta aikata laifi wanda ya saba wa sashi na 287 (7) na laifukan jihar Legas, 2015.
NAN ta ruwaito cewa doka ta tanadar wa mai laifin shekaru bakwai a gidan gyaran hali akan yi wa wanda ya dauke ta aiki sata.
Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 7 ga watan Janairu don ci gaba da shari’ar.
EFCC na neman wasu 'yan Nigeria 4 ruwa a jallo, ta saki hotunansu
A wani labarin, hukumar yaki da rashawa da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, EFCC, ta nemi taimakon 'yan Nigeria wurin neman wasu mutane hudu da ta ayyana nemansu ruwa a jallo kan damfara.
Hukumar a shafinta na Facebook, a ranar Litinin, 22 ga watan Nuwamba ta ayyana neman Akpodemaye Ikolo, Donald Olorunkoyede, Owootomo Tomilola Sunday, da Okuafiaka Bright Onyebuchi ruwa a jallo.
EFCC ta ce ana bincikar wadanda ake zargin ne kan laifuka masu alaka da damfara. Hukumar ta bukaci duk wani da ke da bayani mai amfani dangane da inda mutanen suke ya tuntubi ofisoshinta a kasar.
Asali: Legit.ng