Babban Dalilin mu na kin fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya, Malami

Babban Dalilin mu na kin fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya, Malami

  • Antoni janar na kasa, Abubakar Malami, ya bayyana dalilan da yasa gwamnatin tarayya ta ki fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci
  • Ministan shari'a yace gwamnati na bin komai daki-daki, kuma zata tabbatar ta yi komai a lokacin da ya dace
  • Minsitan ya kuma tabbatar da cewa wannan gwamnatin ba zata kyale ko waye ta gano yana da hannu ba

Abuja - Antoni Janar na kasar nan kuma ministan sharia, Abubakar Malami (SAN) ya bayyana dalilan da yasa gwamnati ke jan kafa wajen fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya.

Malami, wanda ya zanta da kafar watsa labarai ta Channels tv ranar Laraba da yamma, yace ba wai gwamnatin tarayya ba ta son fallasa sunayen bane, tana jiran lokaci ne.

Wannan na zuwa ne duk da matsin lamba da kiraye-kiraye da ake wa shugaban kasa Buhari daga kowane ɓangare kan ya bayyana sunayen mutanen.

Kara karanta wannan

Cire Jumu'a daga ranakun aiki a Kaduna: CAN ta maida martani ga gwamna El-Rufa'i

Abubakar Malami
Babban Dalilin mu na kin fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya, Malami Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Punch ta rahoto Malami yace:

"Abu ɗaya da nake son ku fara duba wa shine har yanzun ana cigaba da bincike, kuma maganar gaskiya mun damke mutane da dama."
"Haka nan kuma mun samu umarnin cigaba da tsare mutanen da muka kama daga sashin shari'a. Kuma babu adalci wani yace ba'a yi komai a kan wannan lamarin ba."
"Har yanzun muna kan bincike. Haka zamu cigaba da kasancewa muna bincike kuma tabbas zamu yi abinda ya dace a lokacin da ya dace."

Shin yan Najeriya ne kaɗai ke wannan aika-aika?

Ministan ya ƙara da cewa sunayen dake hannunsu ya kunshi yan cikin kasa da kuma sanannu da aka sani a kasashen duniya.

Bugu da kari yace gwamnati ta damke su kuma ba zata yi ƙasa a guiwa ba wajen sauke nauyin da yan Najeriya suka dora mata.

Kara karanta wannan

2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai

Ministan ya sha alwashin cewa babu wanda gwamnati zata ɗaga wa kafa ko shi waye sai ya girbi abinda ya shuka.

A wani labarin kuma mun kawo muku Yadda Yan daba suka kai hari ofishin jam'iyyar APC na tsagin Shekarau a Kano

Wasu gungun yan daba sun kai hari ofishin jam'iyyar APC na tsagin tsohon gwamna, sanatan Kano ta tsakiya, Malam Shekarau.

Rahoto ya nuna cewa yan daban sun kai wannan hari ne da yammacin Ƙaraba, inda suka kona sakateriyar dake hanyar Maiduguri a Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262