UK ta fitar da sabbin shawarin tafiye-tafiye, ta ja kunne kan jihohi 12 na Najeriya

UK ta fitar da sabbin shawarin tafiye-tafiye, ta ja kunne kan jihohi 12 na Najeriya

  • Gwamnatin Ingila ta ja kunnen mutanen kasar ta da kakkausar murya kan tafiye-tafiye zuwa wasu jerin jihohi a Najeriya
  • Kamar yadda ofishin FCDO ya sanar a wata takarda da ya fitar, jerin jihohin akwai kalubalen tsaro kuma 'yan ta'adda na iya sace mutum
  • Jihohin sun hada da Borno, Yobe, Adamawa, Kaduna, Sokoto da jerin wasu jihohin kudancin kasar nan

Gwamnatin Ingila ta shawarci 'yan kasar ta kan ziyara ko tafiye-tafiye zuwa wasu jihohin Najeriya saboda matsalar tsaro.

A wani shawarin tafiye-tafiye da suka saki a ranar Alhamsi, 2 ga watan Disamba, ofishin Foreign, Commonwealth & Development, FCDO, ya shawarci 'yan kasan a kan ziyara zuwa jihohi kamar haka:

UK ta fitar da sabbin shawarin tafiye-tafiye, ta ja kunne kan jihohi 12 na Najeriya
UK ta fitar da sabbin shawarin tafiye-tafiye, ta ja kunne kan jihohi 12 na Najeriya. Hoto daga Christopher Furlong
Asali: Getty Images
  1. Borno
  2. Yobe
  3. Adamawa
  4. Gombe
  5. Kaduna
  6. Katsina
  7. Zamfara
  8. Delta
  9. Bayelsa
  10. Rivers
  11. Akwa Ibom
  12. Cross River

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Kotu ta sake sakin jagoran kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu a zaman shari’ar yau

FCDO ta rubuta:

"Akwai yuwuwar 'yan ta'adda su kaddamar da farmaki a Najeriya. Da yawa daga cikin hare-haren 'yan Boko Haram ne ko kuma Islamic State West Africa (ISWA ke yi a jihohin Borno, Yobe da Adamawa da ke arewa maso gabas.

"Tuni kungiyoyin sun nuna niyya da kuma cewa za su iya garkuwa da mutane a Najeriya. Baki da suka hada da masu ayyukan jin kai su ne aka fi sacewa."

Ta kara da shawartar jama'a kan tafiya zuwa jihohin nan sai dai idan akwai kwakwaran dalili. Sun hada da:

  1. Bauchi
  2. Kano
  3. Jigawa
  4. Niger
  5. Sokoto
  6. Kogi
  7. Kilomita ashirin kusa da iyakar Nijar a Kebbi
  8. Abia
  9. Yankunan da babu ruwa na jihohin Delta, Bayelsa da Ribas

ISWAP sun saci fasinjoji 15 a Borno, sun iza keyarsu cikin dajin Sambisa

A wani labari na daban, A kalla fasinjoji 15 ne miyagun da ake zargin mayakan ta'addancin ISWAP ne suka sace a Borno. Wata majiya ta sanar da Daily Trust cewa, an sace jama'ar ne a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Kara karanta wannan

Ka ceto 'yan Najeriya daga yunwa da rashin tsaro, Agbekoya ga Buhari

Majiyar ta ce 'yan ta'addan sun kai farmaki ne wurin kauyen Gumsuri da ke karamar hukumar Damboa ta jihar.

Ya ce sun tare masu ababen hawa inda suka saka karfi wurin tasa keyarsu zuwa dajin Sambisa. Najeriya Daily Trust ta tattaro cewa, akwai wasu daga cikin ma'aikatan kungiyoyin taimakon kai da kai daga cikin wadanda aka sacen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng