Bayan Abinda Ya Faru, Gwamnatin Ganduje Ta Dakatar da Sufurin Jiragen Ruwa a Bagwai
- Gwamnatin Kano ta sanar da ɗaukar matakin dakatar da sufurin jiragen ruwa a yankin karamar hukumar Bagwai
- Rahoto ya nuna cewa a zaman majalisar zartarwa, gwamnatin ta kafa kwamitin da zai binciko musabbabin hatsarin da ya lakume sama da rai 20
- Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jajantawa al'ummar Kano musamman iyalan waɗan da aka gano sun mutu
Kano - Gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Dakta Abdullahi Ganduje, ta dakatar da zirga-zirgan jiragen ruwa a karamar hukumar Bagwai.
Gwamnatin ta ɗauki wannan matakin ne a taron majalisar zartarwa da ya gudana ranar Laraba a gidan gwamnatin jiha.
BBC Hausa ta rahoto cewa wannan na zuwa ne awanni 24 bayan jirgin ruwa ya yi hatsari a yankin ranar Talata, mutane da dama suka mutu.
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Muhammad Garba, shine ya sanar da haka jim kaɗan bayan taron, yace gwamnati zata samar da mafita.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wane mataki gwamnatin zata ɗauka?
Kwamishinan ya bayyana cewa gwamnatin jihar zata samar da motocin Bas da zasu rinka zirga-zirga da jigilar mutane kyauta a yankin.
A cewarsa, gwamnatin zata samar da motocin Bas ɗin guda biyu ne a yanzu, kuma zasu rinka aiki daga Hayin Badau zuwa Bagwai.
A cikin jawabinsa, yace:
"Za'a cigaba da jigilar mutane da waɗan nan motoci, har zuwa lokacin da gwamnati zata samar da jiragen ruwa ga al'umma."
Hakanan kuma a zamanta na ranar Laraba, majalisar zartarwar Kano ta kafa kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike kan musabbabin nutsewar jirgin.
Shugaba Buhari ya jajanta wa mutanen Kano
Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya jajantawa gwamnati da mutanen jihar Kano, musamman iyalan sama da mutum 20 da aka tabbatar sun mutu.
Buhari ya kara da cewa gwamnatin tarayya zata cigaba da bada taimakon da ake bukata yayin da ake cigaba da aikin ceto sauran mutanen.
A wani labarin kuma Ganduje ya yi magana kan daliban Islamiyya 20 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kano
Ganduje ya roki matukan jirgin ruwa su daina cika wa abun hawan su kaya har ya fi ƙarfinsa, domin rayuwar mutane ce a gaba.
Ya kuma yi addu'ar samun rahamar ubangiji ga waɗan da suka mutu, tare da fatan samun lafiya ga waɗan da ke kwance a Asibiti.
Asali: Legit.ng