Babbar Magana: Rikici ya barke, yan Acaba sun lakadawa yan sanda dukan tsiya a Legas

Babbar Magana: Rikici ya barke, yan Acaba sun lakadawa yan sanda dukan tsiya a Legas

  • Hukumar yan sanda ta gurfanar da wasu yan acaba a gaban kotun majistire bisa zargin lakaɗawa jami'anta duka da kuma lalata motocin sintiri
  • Ɗan sanda mai gabatar da ƙara, ya shaida wa kotun cewa yan acaban da sauran abokan aikinsu sun bar yan sanda biyu da jinya a Asibiti
  • Sai dai a nasu ɓangaren, mutanen da ake zargin sun musanta tuhumar da ake musu, kotu ta ba su beli bisa sharuɗɗa

Lagos - A ranar Laraba an gurfanar da wasu yan acaɓa biyu, Jimoh Lasisi mai shekara 43 da Femi Ajayi mai shekara 35 bisa zargin lakaɗa wa jami'an yan sanda dukan tsiya.

Daily Nigerian ta rahoto cewa an gurfanar da mutanen biyu ne a gaban wata kotun Majistire dake jihar Legas, kuma ana zargin sun ƙona motocin sintiri biyu.

Kara karanta wannan

'Karin bayani: Gwamnatin Kano tare da 'yan sanda sun rufe lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau da wasu mutane a cikin ofishinsa

Ana tuhumar yan acaɓan guda biyu kan abubuwa huɗu, da suka haɗa da haɗin kai, cin mutuncin yan sanda da kuma tada zaune tsaye.

Rikicin yan sanda
Babbar Magana: Rikici ya barke, yan Acaba sun lakadawa yan sanda sukan tsiya a Legas Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Sai dai a ɓangaren waɗan da ake zargin, sun musanta aikata abubuwan da ake tuhumarsu da shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yaushe suka aikata laifukan?

Mai gabatar da ƙara, Benedict Aigbokhan, ya faɗa wa kotun cewa waɗan da ake zargin da kuma wasu yan acaban da suka tsere sun aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Nuwamba da 25 ga watan Nuwamba a Jakande Estate Gate.

Ya kuma kara da cewa waɗan da ake zargin sun haɗa kai wajen raunata yan sanda guda biyu yayin da suke bakin aiki.

Mai gabatar da karan yace jami'an da aka lakaɗawa dukan sune, Alulu Tunde da Wasiu Isiaka, kuma dukan su suna aiki ne a caji ofis ɗin Ejigbo.

Kara karanta wannan

Dubun wasu gawurtattun yan bindiga 32 ya cika, yan sanda sun kwato muggan makamai

Hakanan kuma Aigbokhan ya shaidawa kotun cewa waɗan da ake zargi da abokan aikin su, sun lalata motocin sintiri guda biyu.

Yace laifin da suka aikata ya saba wa sashi na 44, 170(3), 250 da 411 na kundin dokokin manyan laifuka na jihar Legas, 2015.

Wane mataki kotu ta ɗauka?

Aminiya Hausa tace Alkalin kotun, mai shari'a E. O. Ogunkanm, ya baiwa waɗan da ake zargin beli a kan N500,000 kowanen su, da kuma waɗan da zasu tsaya musu.

Hakanan ya kuma kafa musu sharuɗɗan cewa wajibi waɗan da zasu tsaya musu su kasance ma'aikatan gwamnati, kuma su gabatar da shaidar biyan haraji ga gwamnatin jihar Legas.

A wani labarin na daban kuma Ganduje ya yi magana kan daliban Islamiyya 20 da suka mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kano

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana rashin jin daɗinsa bisa hatsarin jirgin ruwa da ya faru a Kano.

Kara karanta wannan

Abun Tausayi: Yadda wata mahaifiya ta sadaukar da rayuwarta domin ɗanta ya tsira

Ganduje ya roki matukan jirgin ruwa su daina cika wa abun hawan su kaya har ya fi ƙarfinsa, domin rayuwar mutane ce a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262