Matata ke fara bani haƙuri ko da ba laifinta bane; Mijin matar da ta gama digiri da 1st Class

Matata ke fara bani haƙuri ko da ba laifinta bane; Mijin matar da ta gama digiri da 1st Class

  • Mijin wata mata mai yara uku da ta kammala jami’ar jihar Ilorin da sakamako mafi daraja ya ce nasararta ba abar mamaki bace a wurinsa
  • Mijin matar wanda malami ne a jami’ar ya yaba wa matarsa akan kokari da jajircewarta a gidan aurensu da kuma makaranta
  • Mr Omotosho ya bayyana yadda matarsa take a gidansa inda ya ce tana da saukin kai kwarai da gaske don ita take fara ba shi hakuri idan su ka yi fada

Wata mata mai yara uku tana daya daga cikin dalibai kadan da su ka kammala jami’ar jihar Ilori da sakamako mafi daraja a taron yayen dalibai da aka yi.

Mrs Omotosho ta samu nasarar da wasu daliban marasa aure ba su samu ba yayin da take karatu a fannin jinya, kuma ta kammala bayan haihuwar jaririnta da sati biyu.

Kara karanta wannan

A cikin shekaru 3, motoci 30 na sata, Wanda ake zargi da fashi da makami

Matata ta kan bani haƙuri ko da bata da laifi; Mijin matar da ta gama digiri da 1st Class
Matar tana da 'ya'ya uku, ga aure kuma daliba ce
Asali: Original

Ya yi bayani akan dalilin da yasa bai yi mamakin nasararta ba

Tana daya daga cikin dalibai masu hazaka a jami’ar kuma ta dade tana wakiltar jami’ar a gasa daban-daban da ake yi don haka mijinta bai yi mamakin nasararta ba.

Mijinta, wanda malami ne a jami’ar jihar Ilorin din ya bayyana yadda dama ya san dama zata samu nasarar kuma ya ce yana matukar alfahari da ita saboda tun saninshi da ita tana da hazaka.

Aikin mutane uku take yi a lokaci guda

Kamar yadda ya sanar da Legit TV:

“A shirye nake da in yi mata komai saboda macece mai saukin hali da biyayya. Ina alfaharin sakamakonta mai kyau.”

Tana aikin da ya kamata mutane uku su yi lokacin tana makaranta tana kula da jaririnta mai makwanni biyu da haihuwa, ta na yin bireda kuma tana da shagon da take sayarwa mutane kayan biredi.

Kara karanta wannan

Yan bindiga da Sojojin sun yi musayar wuta a Imo kan umarnin zama a gida na IPOB

Yayin da yake yaba wa matar tasa ya ce bata da son jiki kuma tana da saukin hali da biyayya. Tana jajircewa akan karatunta.

Yanzu haka Mr Omotosho ya na kammala digirinsa na digirgir ne inda yace ba ya taba hassada da nasarorin da matarsa kuma ya ce yana so ta kai irin matakin karatunsa.

A cikin makaranta ba sa magana da juna

Mrs Omotosho ta yaba wa mijinta akan kokarinsa akan karatunta.

Duk da kasancewar su na da aure, ba sa kula juna a makaranta don kawai ta samu ta mayar da hankalinta a karatu.

Mijin ya musanta batun samun nasararta da kasancewa malami a makarantar inda yace kokarinta ne ya sama mata nasara.

Kalla bidiyon a kasa:

Zugar Ƙawaye Na Bi: Ku Taya Ni Roƙon Mijina Ya Mayar Da Ni, Tsohuwar Matar Babban Sarki a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Olori Damilola, tsohuwar matar Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ta fito fili ta bai wa basaraken da gidan sarautar hakuri.

Kara karanta wannan

Ba Zata Saɓu Ba: Ba Za Mu Amince Da Haramtawa Mata Musulmi Saka Niqabi Ba a FUNAAB, In Ji MURIC

A wata takarda wacce ta wallafa ta shafin ta na Instagram a ranar Lahadi, sarauniyar ta bai wa gabadaya ‘yan uwan Adeyemi hakuri da kuma majalisar jihar Oyo.

Damilola, wacce ita ce amaryar basaraken, ta zargi gidan sarautar da nuna halin ko-in-kula akan ta da dan ta daya tal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164