Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi birnin Dubai yau Laraba don halartan taron baja koli
- Bayan yan makonni da dawowa Najeriya, Buhari zai tafi birnin Dubai don halartan taro
- Shugaban kasa zai samu rakiyar ministoci kimanin mutum 10, Ministan tsaro da kuma sauran jami'an gwamnati
- Shugaba Buhari zai gana da manyan Sarakunan kasar UAE tare da Babban Hafsan Sojin kasar
Birnin tarayya - Shugaba Muhammadu Buhari zai shilla birnin Dubai, haddadiyar daular Larabawa, ranar Laraba domin halartan taron baja kolin EXPO 2020.
Wannan taron baja koli zai auku ne ranar Juma'a, 3 ga watan Disamban 2021.
Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki kuma Legit ta samu.
Shugaban zai samu rakiyar ministoci da jami'an gwamnati sama da 10.
Adesina ya bayyana cewa Shugaba Buhari zai gana da Sarkin Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum, da kuma Yarima mai jiran gadon masarautar Abu Dhabi Mohamed bin Zayed Al Nahyan.
'Karin bayani: Gwamnatin Kano tare da 'yan sanda sun rufe lauyan da ya wakilci bangaren Shekarau da wasu mutane a cikin ofishinsa
Adesina yace:
"Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja yau Laraba don halartan EXPO 2020 Dubai, haddadiyar daular Larabawa."
"Bayan yawon duba sashen kayan Najeriya ranar Juma'a, shugaban kasan zai karbi bakuncin yan kasuwa da kuma Yarima mai jiran gadon Abu Dhabi, Mohamed bin Zayed Al Nahyan, da kuma mataimakin kwamandan Sojin UAE da Sarkin Dubai kuma mataimakin Firai Minista, Sheikh Mohammed bin Rashid Al Maktoum."
"Shugaban kasan zai dawo Abuja ranar Lahadi, 5 ga Disamba, 2021."
Da wa zai tafi?
Adesina ya ce Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje Geoffrey Onyeama; Ministan masana'antu, kasuwanci da zuba hannun jar, Otunba Adeniyi; Ministar Kudi, Hajia Zainab Shamsuna; da Ministan Noma da cigaban karkara, Dr Mouhammad Abubakar.
Hakazalika akwai Ministan Sufurin sama, Hadi Sirika; Ministan Lafiya, Dr Osagie Ehanire; Ministan Sadarwa, Dr Isa Ali Pantami; Ministan karafuna da ma'adinai, Olamilekan Adegbite; da karamar ministan zuba jari, Amb Maryam Katagum.
Sauran sune Ministan Tsaro, Bashir Salihi Magashi; NSA Babagana Monguno; Dirkata Janar na NIA, Amb Ahmed Rufa'i Abubakar da Shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.
Asali: Legit.ng