Kudin danyan man fetur N2tr da aka haka a 2019 sun yi batan dabo

Kudin danyan man fetur N2tr da aka haka a 2019 sun yi batan dabo

  • Ofishin Odito-Janar na tarayya ta zargi NNPC kan batan wasu kudaden danyen man fetur da akayi a 2019
  • Kudin Gangan danyen mai 104.48 million da ya bacen zai kai N2 trillion
  • A 2019, Gwamnatin tarayya ta yi kasafin kudin N8.83trn kuma bashi aka karba daga kasashen waje

An yi zargin kamfanin man feturin Najeriya NNPC bai yi bayanin yadda aka yi da gangan mai milyan 104.48 da aka haka ba a shekarar 2019.

Wannan na kunshe cikin lissafin da Dataphyte tayi inda tayi amfani da rahoton NNPC na shekara da kuma rahoton ofishin Odito-Janar.

A rahoton, NNPC ta haki mai ganga milyan 107.24, amma ganga milyan 2.76 kawai aka bada kudinsu.

Nawa suka yi batan dabo?

Kara karanta wannan

Litar man fetur zai zarce N340 a farkon shekarar 2022 idan gwamnati ta cire tallafi - ‘Yan kasuwa

Rahoton ofishin Odito-Janar da Legit.ng ta gani ya nuna cewa an sayar da gangar mai guda milyan 2.76 a farashin N55.89 billion.

Amma babu bayani kan yadda aka sayar da sauran ganguna miliyan 104.48.

Da akayi lissafin kudin gangar mai milyan 104.48 a farashin $64.3 ga gangan a 2019, kudin ya kai $6.64 billion(N2.7 trillion).

Odito Janar yace:

"Ba'a bada bayani kan danyan mai da matatun mai ba suyi amfani da su ba, kuma ba'ayi bayani kan adadin danyen man da aka fitar tsakanin 30 ga Mayu zuwa Disamba 2019 ba."

Kudin danyan man fetur N2tr da aka haka a 2019 sun yi batan dabo
Hoto: Dataphyte
Kudin danyan man fetur N2tr da aka haka a 2019 sun yi batan dabo
Asali: Facebook

Rahoton Dataphyte ya kara da cewa irin haka ya sake faruwa a 2011 lokacin da NNPC ta gaza bayani kan gangar mai 65,000 cikin ganga 445,000 da ake fitarwa kullum.

Kara karanta wannan

FG ta zargi ESN da yanka wasu ‘yan sanda tare da yada bidiyon gawarwakinsu a intanet

Wannan ya haifarwa Najeriya asarar N1.033 billion kulli yaumin kuma N31.005 billion a wata.

Menene illan haka

Da an zuba kudin wannan danyen man da sukayi batan dabo, da Gwamnati ba zata bukaci karban wasu basussuka da ta karba ba.

Kawo 30 ga Yuni, 2021, bashin da aka bin Najeriya ya kai N35.5 trillion.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng