Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko

Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko

  • Babban alkalin Najeriya, CJN Tanko Mohammed ya sanar da cewa fannin shari'ar kasar nan ba zai huta ba har sai ya ga karshen rashawa
  • Tanko ya ce fannin shari'ar a kasar nan a cikin shekara biyu kacal an yi shari'a da yawan ta ya kai 756 duk da ke da alaka da rashawa
  • A cikin watanni 11 na wannan shekarar kuwa, Tanko ya ce an yanke hukunci kan mutum 1,144 da ke alaka da rashawa, an kwace jirage sama takwas da gidajen mai 7

Shugaban alkalan Najeriya, Tanko Mohammed, ya sha alwashin cewa fannin shari'ar kasar nan ba za ta huta ba har sai ta ga bayan rashawa a kasar nan.

Shugaban alkalan ya sanar da hakan ne a ranar Talata yayin taron ganin bayan rashawa a kasar nan inda yayi jawabi a Abuja, babban birnin kasar, Channels TV ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ayyuka 257 aka kwafo daga kasafin kudin 2021 masu darajar N20bn, ICPC

Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko
Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko. Hoto daga dailynigerian.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda yace, tsakanin shekarar 2020/2021, an yi shari'ar da ta danganci rashawa 756 a kasar nan.

Ya kara da cewa, daga watan Janairu zuwa Nuwamban shekarar nan, wadanda ake zargi 1,144 aka yanke wa hukunci kan laifukan rashawa da makamantansu wanda ya hada da kwace daruruwan miliyoyi, jiragen sama takwas, gidajen mai bakwai da sauransu.

Mohammed ya yi kira da ga alkalai kan su cire tsoro ko wariya kuma su yi hukunci kamar yadda ilimin shari'a ya tanadar, Channels Tv ta ruwaito.

Ya kara da cewa, dukkan kasar da ke son cigaba, dole ne fannin shari'a ta zama mai zaman kanta kuma babu abinda ke iya girgiza ta tun daga kan kudi zuwa sauransu.

Shugaban alkalan a watan Nuwamban ya yi kira ga alkalai da su tashi tsaye kan dukkan kalubalen tare da dawowa da 'yan Najeriya kwarin guiwa da tabbacinsu a fannin shari'a.

Kara karanta wannan

2023: Nnamdi Kanu ya raunana yuwuwar samar da dan takara nagari daga kudu maso gabas, Yakasai

Ya ce dole ne alkalan su tabbatar da adalci ba tare a ga alkalan kasar nan da su kiyaye tare da gujewa bada hukunci ko kangewa kafin a yanke hukunci domin gujewa bata sunan fannin shari'a.

Jerin sunayen alkalai 22 da CJN ya rantsar na babban birnin tarayya

A wani labari na daban, babban alkalin Najeriya, CJN Ibrahim Tanko Muhammad, a ranar Talata ya rantsar da sabbin alkalan babban kotun tarayya ta Abuja har guda 22.

Tanko ya yi kira garesu da su guje wa duk abinda suka san zai bata musu suna, Daily Nigerian ta ruwaito.

Babban alkalin yayin rantsar da alkalan a kotun koli da ke Abuja, ya yi kira garesu da su runtse idanuwansu kan duk wani abu da zai rude su ko kuma abinda zai kange su daga kaiwa kololuwar aikinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng