Da duminsa: An damke Fani-Kayode a kotun Legas, EFCC ta tafi da shi ofishin ta

Da duminsa: An damke Fani-Kayode a kotun Legas, EFCC ta tafi da shi ofishin ta

  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta damke Femi Fani-Kayode a cikin babbar kotun tarayya da ke Ikoyi ta jihar Legas
  • Bayan an kammala zaman kotu a yau Talata kan zarginsa da ake da laifuka 17, mai bincike na hukumar EFCC ya tare shi tare da tasa keyarsa
  • Kamar yadda mai binciken ya sanar, ya ce an garzaya da tsohon ministan sufurin jiragen saman ofishinsu mafi kusa domin amsa tambayoyi

Legas - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta damke Femi Fani-Kayode, jigon jam'iyyar APC.

An damke shi a wata babbar kotun tarayya ce da ke zama a Ikoyi, jihar Legas kuma an tafi da shi ofishin hukumar EFCC mafi kusa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Ranar Litinin zamu dawo da Sabis jihar Zamfara, Matawalle

Tsohon ministan, wanda aka gurfanar a gaban kotu kan takardun bogi, ya na kokarin fita daga kotun ne bayan an dage shari'ar zuwa ranar 24 ga watan Janairun shekara mai zuwa, yayin da mai binciken EFCC ya dumfare sa.

Da duminsa: An damke Fani-Kayode a kotun Legas, EFCC ta tafi da shi da shi ofishin ta
Da duminsa: An damke Fani-Kayode a kotun Legas, EFCC ta tafi da shi da shi ofishin ta
Asali: Original

Daga nan ne aka kama shi tare da yin awon gaba da shi zuwa ofishin hukumar, mako daya kenan bayan wancan kamen, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Mai binciken na hukumar EFCC, Shehu Shuaibu, ya ce ana tuhumar tsohon ministan sufurin jiragen saman ne kan wasu takardun bogi.

Hukumar yaki da rashawan ta shirya tuhuma kan zargi 17 na halasta kudin haram da suka kai N4.6 biliyan kan Fani-Kayode tare da tsohon karamin ministan kudi, Nenandi Usman.

A tare da wadanda ake zargin akwai Yusuf Danjuma, tsohon shugaban kungiyar shugabannin kananan hukumomi da kamfanin Jointrust Dimentions Nigeria Ltd.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da DPO na yan sanda

Wanda ake zargin ya gurfana a gaban Mai shari'a Mohammed Aikawa na babbar kotun tarayya da ke Legas, kuma ya musanta aikata dukkan laifukan sannan an bayar da belinsa.

An fara shari'ar a gaban Mai shari'a Aikawa da kuma shaidun da aka gabatar, sai dai yanzu Aikawa ya bar kotun yankin Legas.

Daga bisani an mika shari'ar zuwa sabon alkali, Mai shari'a Daniel Osaigor kuma an shirya kan cewa za a sake gurfanar da wadanda ake zargi a ranar 13 ga watan Oktoban 2021.

Amma a ranar da aka yi za a cigaba da shari'ar, Fani-Kayode tare bai halarci kotun ba, sai dai lauyansa ya sanar da kotun cewa an kwantar da shi a babban asibitin gwamnati da ke Kubwa a Abuja.

Ya bukaci a dage sauraron shari'ar saboda rashin lafiyar a madadin wanda ya ke karewa. Sai dai mai gurfanar da shi ta EFCC, Bilkisu Buhari, ta sanar da kotun cewa wanda ke kare kansa ya saba yin amfani da irin wannan salon a duk lokacin da ba ya son halartar kotu.

Kara karanta wannan

Shugaban karamar hukuma a Kano ya fada hannun ICPC, ana zargin ya ci makudan kudi

Bayan dubawa, Mai shari'a Osiagor ya ce tabbas wanda ake zargin ya taba kawo irin wadannan uzirin har sau biyar.

Kotun daga nan ta umarci wanda ke kare kansan da ya bayyana gaban kotu a zama na gaba ba tare da wani uziri ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng