Da Dumi-Dumi: Kotu ta ce korar Sarki Sanusi daga Kano ya saɓa doka, ta umurci Ganduje ya biya shi tarar N10m
- Babban kotun tarayya ta Abuja ta yanke hukunci kan korar Sarki Muhammadu Sanusi II daga Kano bayan tsige shi
- Mai shari'a Anwuli Chikere yayin yanke hukuncin ya ce dokar da gwamnatin jihar Kano ta yi amfani da shi ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa
- Alkalin kotun ya ce duk wata doka da ta ci karo da na kasa watsi da ita ake yi, ya kuma umurci gwamnatin ta biya Sanusi II diyyar N10m
Abuja - Wata babban kotun tarayya da ke Abuja, a ranar Talata, ta yanke hukunci cewa korar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga jihar Kano ya saba wa doka da kudin tsarin mulki, Daily Nigerian ta ruwaito.
Mai shari'a Anwuli Chikere, cikin hukuncin, ya jadadda cewa Dokar Masarauta ta 2019 da gwamnatin jihar ta yi amfani da shi wurin korar Sanusi ta ci karo da kudin tsarin mulkin Nigeria ta 1999 da aka yi wa kwaskwarima.
A cewar Chikere, kundin tsarin mulkin Nigeria ta fi kowanne doka karfi don haka duk dokar da ta ci karo da ita za a yi watsi da ita ne, The Nation ta ruwaito.
Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, ta ruwaito cewa Mr Sanusi, wanda aka tsige a ranar 9 ga watan Maris din 2020, ya yi karar Sufeta Janar na yan sanda da shugaban SSS, a ranar 12 ga watan Disambar 2020 kan 'tsare shi ba bisa ka'ida ba'.
A karar da ya shigar mai lamba FHC/ABJ/CS/357/2020, ya kuma yi karar Antoni Janar na Jihar Kano da Antoni Janar na kasa.
Sanusi bai kallubalanci tsige shi ba
Duk da cewa Mr Sanusi bai kallubalanta tsige shi da aka yi ba, ya shigar da kara kotu inda a tabbatar masa da damarsa na zuwa duk inda ya ke so.
Ya kuma kallubalanci wadanda ya yi karar saboda cin fuska da keta masa hakkinsa na dan adam.
Mai Shari'a Chikere, wanda ya cire sunan Antoni Janar na kasa daga karar, ya bukaci sauran wadanda aka yi karar su dena cin mutuncin Sanusi.
Kotu ta ce a biya Sarki Sanusi II diyyar N10m
Har wa yau, kotun ta umurci wadanda aka yi karar su biya Sarki Sanusi II diyyar Naira miliyan 10 sannan su nemi afuwarsa a wallafa a manyan jaridu na kasa guda biyu.
Asali: Legit.ng