Shekaru 8 da kashe Sheikh Albani Zaria, an cika masa burinsa na kafa gidan talabijin
- Cibiyar Daarul Hadeethis Salafiyyah ta kafa gidan talabijin na musamman domin yada da’awarta
- Tashar Albaniy TV za ta fara aiki a farkon shekarar 2022, abin da Marigayi Albani Zaria ya ci buri
- Daarul Hadeethis Salafiyyah ta na karantar da musulunci da kiran a komawa karantarwar magabata
Kaduna - Kungiyar Daarul Hadeethis Salafiyyah da ke garin Zaria, jihar Kaduna ta kafa gidan talabijin na musamman domin yada karatun addinin musulunci.
Legit.ng Hausa ta samu labari cewa sabon tashar Albaniy TV za ta fara aiki ne a watan Junairun shekarar 2022, a halin yanzu an kammala duk wasu shirye-shirye.
Ga masu neman kamo wannan tasha a tauraron ‘Dan Adam, sai su yi harin tauraron “Amos a digiri 17º daga gabas a mita 11753, za su karkata kan na’urarsu a tsaye.
Daya daga cikin jagorori kuma malaman wannan cibiyar addini, Dr. Kabir Abubakar wanda aka fi sani da Sheikh Asgar, ya tabbatar da wannan a shafinsa na Facebook.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Za a fara kallon Albaniy TV a Junairun 2020 in sha Allah
Cibiyar ilimi ta Daarul Hadeethis Salafiyyah dake Zariya a jihar Kadunan Nijeriya ta gama shiryarwa tsaf don fara watsa shirye-shiryen talabijin din ta mai suna Albaniy TV akan tauraron dan Adam.
Wannan gidan TV daya ne daga cikin hanyoyin yaɗa da'awa da inganta ta waɗanda marigayi Malam Albani Zaria ya ci burin kafawa.
Allah cikin ikonsa, ya cika masa wannan buri bayan rasuwar sa da shekaru 8 ta hannun dalibansa wadanda suka ci gaba da gudanar da cibiyar da ya bari a matsayin sadakatul jariya.
Cikin taimakon Allah, Shugaban cibiyar watau Farfesa Abdurrafii abdulganiyyi da sauran mataimakansa sune suka samar da tashar talabijin ɗin. – Kabir Asgar.
Asgar yace za a rika sa karatun addini da sauran shirye-shiryen da za su fadakar da al’umma a kan addini da harkokin duniya a tashar a harsunan Hausa da Ingilishi.
A wani bidiyo da yake kan shafin gidan talabijin, sun fara kira ga masu neman tallata kasuwancinsu da su kawo hajarsu, muddin bai saba addini ko al’ada ba.
Burin Marigayi Sheikh Albani Zaria
A lokacin da malamin da ya assasa wannan kungiya, Albani Zaria yake raye, yace bai da burin da ya wuce ya a saurari karatunsa a gidan talabijin da cibiyarsa za ta kafa.
Kafin a kashe shi a farkon shekarar 2014, Sheikh Auwal Adam yace idan Allah ya so za a kafa wannan talabijin, yace amma Allah kadai ya san yaushe hakan zai tabbata.
Asali: Legit.ng