Almajiranci ke ruruta wutan rashin tsaro a Arewacin Najeriya, Bishop Onaiyekan
- Babban Malamin addinin Kirista ya bayyana daya daga cikin abubuwan da suka haddasa matsalar tsaro a Najeriya
- Onaiyekan ya bayyana cewa da yawa cikin yaran dake zama yan bindiga Almajirai ne da iyayensu sukayi watsi da su
- Gwamnonin Arewacin Najeriya sun haramta Almajiranci a fadin yankin gaba daya
Abuja - Tsohon Shugaban Cocin Katolikan Abuja, Cardinal John Onaiyekan, ranar Asabar ya bayyana cewa Almajiranci ne abinda ke ruruta wutan matsalar tsaro a Arewacin Najeriya.
Onaiyekan ya bayyana cewa yaran da iyayensu suka mance da su shekarun baya ne suka zama yan ta'addan Boko Haram.
Punch ta ruwaito cewa Cardinal John Onaiyekan ya bayyana hakan ne a Abuja yayin taron kaddamar da fim dake wayar da kai kan kananan yara marasa gata.
A cewarsa:
"Muna da babbar matsala yanzu a Arewa na Almajiranci. Wadannan kananan yara ne musamman wadanda iyayensu suka yi watsi da su. Mun san da yawa cikinsu sun zama yan Boko Haram."
"Shekaru goma da suka wuce, wadannan yan ta'adda yara ne, amma yau sun zama matasa marasa aikin yi, saboda haka shirya suke suyi komai."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Gashi yau muna fama, kuma wannan shine dalilin da yasa abin ya tsananta."
Sarkin Musulmi: Almajiranci Da Yawon Barace-Barace a Tituna Ba Musulunci Bane
Sarkin musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi kira akan amfani da ilimin addinin musulunci da na zamani wurin kawo karshen almajirci a arewacin Najeriya.
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, ya yi wannan jawabin ne a ranar kammala wani taro da suka kwashe kwana 2 suna yi akan hanyoyin inganta ilimin Almajirci a jihar Sokoto.
Abubakar ya ce wajibi ne masarautar da sauran su hada kai wurin kawo ci gaba wanda zai kawo karshen barace-barace a jihar Sokoto da arewacin Najeriya gabadaya.
Basaraken ya yi jawabin inda ya ce shi da sauran mutane da dama sun yi ilimin almajirci saidai sun yi shi ne don neman ilimin addini da larabci ba bara ba.
Asali: Legit.ng