Ba Zata Saɓu Ba: Ba Za Mu Amince Da Haramtawa Mata Musulmi Saka Niqabi Ba a FUNAAB, In Ji MURIC
- Kungiyar kare hakkin musulmai, MURIC ta nuna rashin amincewarta karara akan hana mata sa Niqabi a jami’ar tarayya da ke jihar Ogun ta FUNAAB
- An samu bayanai akan yadda jami’an tsaron jami’ar su ka tilasta wata wacce ta kammala jami’ar cire niqabi daga fuskarta kafin su bar ta ta shiga cikin makarantar
- Hakan yasa darektan MURIC, Ishaq Akintola a ranar Lahadi ya saki wata takarda cike da alhinin lamarin inda ya ce kowa yana da damar yin shigar da addininsa ya yarda da ita
Ogun - Kungiyar kare hakkin musulmai, MURIC ta nuna rashin amincewarta da hana sa niqabi ga matan musulmai da hukumar Jami’ar Noma ta Tarayya da ke Abeokuta, FUNAAB ta yi, Daily Nigerian ta ruwaito.
Jami’an tsaron makarantar sun tilasta wa wata mata wacce ta kammala jami’ar cire niqabin da ke sanye a fuskarta sannan su bar ta ta shiga makarantar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yayin mayar da martani akan wannan lamari, darektan MURIC, Ishaq Akintola, a wata takarda ta ranar Lahadi, ya ce kowa ya na da damar yin shigar da addininsa ya yarje masa a duk jami’o’in kasar nan.
Babu makarantar da take da damar hana shigar musulunci
Daily Nigerian ta ruwaito yadda kungiyar tace:
“Babu wata makaranta, tun daga firamare zuwa jami’a, ta jiha ko ta tarayya ko kuma mai zaman kanta da take da damar hana anfani da hijabi ko niqabi. Hakan ya ci karo da sashi na 38(i) da (ii) na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda yace “Ko wanne mutum yana da damar amfani da fahimtarsa da addininsa, da kuma damar sauya addininsa kuma ya yi duk harkokin addinin kamar bauta, koyarwa da ayyuka’.
“Har ila yau a wata takarda ta 18 ta ICCPR ta ba mutum damar yin addininsa ba tare da wani cikas ba.
“Sannan a wata takarda ta 9 na kare hakkin mutane na Europe ta yi nuni da girmama addinin wasu..’ Don haka hukumar FUNAAB ba su girmama addinin musulunci ba. Kuma dole ne a dakatar da hakan.
“Matsalar wasu da ba musulmai ba da ke shugabantar jami’o’in ilimi ko wuraren ayyuka ita ce yadda suke kokarin tilasta musulman da ke karkashin su akan yin shiga da ba ta musulunci ba.”
Dokar FUNAAB ta ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya
Ya kara da cewa cutarwa ne sanya dokakokin da zasu hana musulmai walwala ta hanyar hana su shigar da addininsu ta tanadar.
Akintola ya ce dokar jami’ar ta ci karo da wasu sassani na kundin tsarin mulkin Najeriya. Don haka ba zai yiwu a bi duk wata sanarwa da doka ta hana sa niqabi da FUNAAB ta kafa ba a gaba daya kasar Yarabawa.
Asali: Legit.ng