Bayan shekara 5 an kore shi daga jami'a, ya koma inda ya samu digiri mai daraja ta 1 da lambobin yabo

Bayan shekara 5 an kore shi daga jami'a, ya koma inda ya samu digiri mai daraja ta 1 da lambobin yabo

  • Wani matashi mai suna Timilehin P. Abayomi an kore shi daga jami'a bayan kwashe shekaru biyar ya na karatu amma a yanzu ana murnar kammala digirinsa
  • Timilehin ya koka tare da bada labarin yunkurin kashe kansa da ya yi sakamakon korar shi da aka yi daga jami'ar OAU duk da lokacinsa da ya bata
  • Sai dai daga bisani ya tashi tare da neman gurbin karatu a FUT Akure inda ya kammala da digiri mai daraja ta farko tare da samun lambobin yabo kan kwazonsa

Duk rintsi da tsanani tare da kalubalen da ya fuskanta a baya, wani matashi dan Najeriya ya nuna cewa zai iya inda ya kammala digirinsa.

Timilehin P. Abayomi ya ce an kore shi daga jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife bayan ya kwashe shekaru biyar ya na karatu.

Kara karanta wannan

Dan shekara 78 ya kashe dan'uwansa mai shekaru 94 kan rikicin fili a Ondo

Bayan shekara 5 an kore shi daga jami'a, ya koma inda ya samu digiri mai daraja ta 1 da lambobin yabo
Bayan shekara 5 an kore shi daga jami'a, ya koma inda ya samu digiri mai daraja ta 1 da lambobin yabo. Hoto daga LinkedIn/Timilehin P. Abayomi
Asali: UGC

A wallafar murna da yayi a LinkedIn, Timilehin bai sanar da dalilin da yasa aka kore shi ba amma ya ce hakan ya matukar gigita shi kuma mahaifiyar shi ta dinga kuka.

Ya kusan hakura da karatun

A yayin jin radadin shekarun da ya yi asara a makarantar, matashin ya ce ya dinga yunkurin kashe kansa kuma ya bar gidansu kwata-kwata.

Amma kuma a yayin kokarin ganin ya inganta rayuwarsa, Timilehin ya ce ya yanke shawarar komawa jami'a a shekarar 2015 inda ya zaba jami'ar fasaha ta tarayya da ke Akure.

A yayin wallafa hotuna, Timilehin ya sanar da cewa ya kammala digirinsa da sakamako mai daraja ta farko inda aka bashi wasu lambobin yabo a jami'ar.

Matashin ya ce: "Wannan nasarar daga karshe Ubangiji ne ya bani, shi ya bani ita a karo na biyu, ga mahaifiyata wacce ba ta sare ba, 'yan uwa na wadanda suka yarda zan iya da kuma abokai na da suka kasance tare da ni.

Kara karanta wannan

Martanin yan Najeriya kan wani matashi da ya ci F9 a darussan NECO, Ya kammala digiri da daraja ta farko

"Godiyata ga abokai na uku wadanda suka karfafa min guiwa kuma suka taimaka min - Adesida Thompson, Anjolaolorun Alabi, ACIM & Opeyemi Fawole.
"Wannan labarin na rashin nasara ne a baya, amma ban sare ba. Labari ne na karfin guiwa da dagiya. Idan ka ga wannan labarin, ka yi min addu'ar Ubangiji ya maye min gurbin shekarun da na rasa."

Sabon bidiyon wani mutum ya na tallar fara a cikin jirgin sama ya janyo cece-kuce

A wani labari na daban, bidiyon wani mutum ya na tallar fara a jirgin sama na kasar Uganda kafin ya tashi ya janyo maganganu da yawa a kafafen sada zumunta.

An ga mutumin ya na tallar ga kwastomomi wadanda cike da jin dadi suke ta siyan farar da aka kulla a kananan ledoji yayin da suke mika masa kudi.

Cike da fara'a mutumin ya dinga mu'amala da fasinjojin yayin da ya ke siyar musu da farar. A bidiyon an gan shi ya na kaiwa da kawowa a cikin jirgin ba tare da ma'aikatan jirgin saman sun hana shi ba.

Kara karanta wannan

Labari mai dadi: Sanatoci sun nemi a karawa 'yan NYSC kudin alawus din abinci

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng