Legas: Gobara ta lamushe kayan gyaran ababen hawa na miliyoyin naira a fitacciyar kasuwa

Legas: Gobara ta lamushe kayan gyaran ababen hawa na miliyoyin naira a fitacciyar kasuwa

  • Gagarumar gobara ta lamushe kayan gyaran ababen hawa na miliyoyin naira a fitacciyar kasuwar Ladipo da ke jihar Legas
  • Gobarar da ta fara a daren Lahadi wurin karfe 10:45pm daga wani shagon kafintoci wanda ya gangara har zuwa kasuwar
  • Har a safiyar Litinin, ana kokarin kashe gobarar da wutar lantarki ta haddasa saboda ta kama da wani bene mai hawa 3 a kan titin

Legas - Mummunar gobarar tsakar dare ta lakume kayan miliyoyin naira a fitacciyar kasuwar Ladipo ta siyar da kayayyakin kayan gyara ta Legas.

Daily Trust ta ruwaito cewa, an gano cewa gobarar ta fara ne daga wani shagon kafintoci da ke kan titin Ladipo amma daga bisani ta karasa har wata ma'adanar kayan gyaran Toyota da ke da kusanci da wurin.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Sabuwar kungiyar tsageru ta kai hari kamfanin man fetur a jihar Ribas

DSS ta koka kan yadda 'yan ta'adda ke kitsa yunkurin kai farmaki sansanonin soji
DSS ta koka kan yadda 'yan ta'adda ke kitsa yunkurin kai farmaki sansanonin soji. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyoyi sun ce gobarar ta fara ne sakamakon tartsatsin da wutar lantarki ta yi a shagon kafintocin amma daga bisani ta kai har shago mai lamba 85, Ladipo Street by Fatai Atere way, Ladipo.

Shugaban hukumar NEMA na yankin kudu maso yamma, Ibrahim Farinloye, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya yi bayanin cewa gobarar ta shafi wani bene mai hawa uku kuma ta cigaba har zuwa safiyar Litinin.

Daily Trust ta ruwaito cewa, ya ce har a halin yanzu ginin na ci da wuta kuma babban kalubale ne sakamakon wasu manyan alamu da ya nuna.

Ya ce: "Ginin ya na da kayan gyaran Toyota a ciki. Gobarar ta fara ne daga wani shagon kafintoci da ke kusa da bene mai hawa uku. Ta fara ne daga tartsatsin wutar lantarki wurin karfe 10:45pm na ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta umarci dakatar da hakar man fetur a Bayelsa

"Masu makwabtaka da wurin sun yi ikirarin cewa basu san da tartsatsin da ya haddasa gobarar ba, sun gano ne bayan gobarar ta barke kuma a lokacin ba za su iya shawo kan ta ba.
"Kafin masu kashe gobara su iso, gobarar ta kai har benen mai hawa uku. Har a halin yanzu babu rai da aka rasa kuma ana cigaba da kokarin kashe wutar.
“Jami'an NEMA, LASEMA, masu kashe gobara da 'yan sanda suna wurin domin dakile bata-gari masu satar kayan 'yan kasuwa."

Kano: Gagarumar gobara ta kurmushe a kalla shaguna 41 a kasuwar Kurmi

A wani labari na daban, a kalla shaguna 41 ne suka kurmushe sakamakon gagarumar gobarar da ta tashi a fitacciyar kasuwar Kurmi ta jihar Kano a ranar Litinin, hukumar kashe gobara ta sanar.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kurmi ta na daya daga cikin tsofaffin kasuwannin da ke garin Kano, cibiyar kasuwancin arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Gobara ta sake tashi a wata kasuwar Abuja

Kamar yadda mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar, Alhaji Saminu Abdullahi yace, "Mun samu kiran gaggawa daga wani Malam Baba Nasidi wurin karfe daya da minti hamsin da takwas na dare kan cewa gobara ta tashi a kasuwar litattafai. "

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng