Rundunar soji ta kame jami'anta da suka ci zarafin wasu mazauna a yankin Abuja
- Rundunar sojin Najeriya a wani yankin Abuja ta kame wasu jami'anta bisa laifin cin zarafin wasu mazauna a Abuja
- Hakan ya faru ne a makon jiya, kamar yadda majiya daga yankin ta shaida tare da tabbatarwa manema labarai
- Wani babban jami'in soja ya bayyana cewa, rundunar za ta hukunta sojojin bayan gudanar da cikakken bincike
Abuja - Wani jami’in soji, Kanar Hassan Bawa, ya bayyana cewa an kama wasu sojojin da suka afkawa wasu al’ummar Tungan-Maje a karamar hukumar Gwagwalada a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
Kanar Bawa, wanda aka ce shi ne ya wakilci kwamandan rundunar sojoji, ya yi magana ne a lokacin da ya ziyarci fadar sarkin Tungan-Maje, mai martaba (HRH) Alhaji Salihu Isiaku Na’Annabi, a ranar Alhamis din da ta gabata.
Wata majiya da ke fadar a lokacin da Kanal din sojojin tare da kwamishinan korafe-korafe na FCT Mista Ezikel Dalhatu Musa, ya ce rundunar ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa mazaunan, kuma ta nisanta kanta daga tura wani soja zuwa ga al'umma.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Kuma yayin da yake magana a gaban babban sarkin mu, Kanal din sojan ya fito fili ya musanta cewa ya tura sojoji su kama wani a Tungan-Maje, inda ya ce an kama sojojin da ke da hannu a ciki."
Ya shaida cewa, Kanal din sojojin ya tabbatar wa da sarkin cewa za a hukunta sojojin bayan kammala bincike.
Hakazalika, ya ce Kanal din sojan ya yi alkawarin tura motocin sintiri da babura wadanda za su rika sintiri a yankin domin bincikar faruwar sace-sacen mutane.
Majiyar ta ci gaba da cewa, sarkin ya kai kara ga Kanal din sojan ne bisa zargin bada hayar wani yanki na fili ga wadanda ba ‘yan asalin yankin ba domin noma da sojoji suka yi a wani bariki.
A cewarsa:
“Kuma Kanal din ya yi alkawarin gudanar da bincike a kan lamarin shi ma, duk da cewa ya roki matasa da su daina yada duk wani rashin fahimta da sojoji a shafukan sada zumunta, inda daga bisani ya bayar da shawarar cewa mu rika kiransa a duk lokacin da aka samu matsala da sojoji a barikin."
A baya Sahara Reporters ta rahoto yadda sojojin, wadanda suka kai 13 suka afkawa mazauna yankin, lamarin da ya haifar da tashin hankali
Sojoji sun kame wani babban jami'in IPOB, sun kwato makamai
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya a ranar Alhamis, 25 ga watan Nuwamba ta bayyana cewa ta kama sakataren kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB), Obinna Nwite.
Mukaddashin daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Birgediya-Janar Bernard Onyeuko ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, 24 ga watan Nuwamba.
Nasrun minallah: Jirgin yakin sojoji ya yi luguden wuta kan masu karban haraji na kungiyar ISWAP a Borno
Birgediya-Janar Onyeuko ya ce: “Ayyukan IPOB/ESN a kudu maso gabas sun ragu matuka a ‘yan kwanakin nan.
Asali: Legit.ng