Dan shekara 78 ya kashe dan'uwansa mai shekaru 94 kan rikicin fili a Ondo

Dan shekara 78 ya kashe dan'uwansa mai shekaru 94 kan rikicin fili a Ondo

  • Rikicin fili tsakanin yan uwa biyu a jihar Ogun yayi sanadiyar rashin rai guda daya
  • Jami'an yan sanda sun damke kanin da ya kashe babban yayansa wanda makaho ne kan wannan lamari
  • Ya bayyana dalilin da yasa ya aikita wannan abu kuma ya amsa laifi

Mowe - Wani tsohon dan shekara 78 mai suna Moshood Habibu, ya shiga komar yan sanda bisa laifin hallaka dan uwansa Salisu Surakatu kan rikicin fili a jihar Ogun.

Kakakin yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Asabar, rahoton Channels TV.

Ta bayyana cewa Moshood ya bugawa yayansa sara da adda har lahira ranar Laraba a Mowe, karamar hukumar Obafemi Owode.

Ta ce,

"An damkeshi ne bisa karar da wani Aminu Tajudeen ya shigar ofishin yan sandan Mowe cewa Salisu Surukatu, wanda aka kashe mahaifinsa kuma wanda ya kashe ya shigo gidansu ne a kauyen Kara Ewumi a Mowe inda ya sassareshi kan rikicin fili."

Kara karanta wannan

Bamu ji motsin kowa ba har yanzu, Matar dan a mutun Buhari da aka kashe a jihar Anambra

"Yayinda muka yiwa wanda ake tuhuma tambaya, mutumin ya ce marigayn ya sayar da filin dangi ne kuma ya hana shi nasa kason kuma hakan yasa yaje gidan karba, sai suka kaure da fada."

Dan shekara 78 ya kashe dan'uwansa mai shekaru 94 kan rikicin fili a Ondo
Dan shekara 78 ya kashe dan'uwansa mai shekaru 94 kan rikicin fili a Ondo Hoto:Channels TV
Asali: Facebook

DSP Abimbola tace bincike ya nuna cewa kanin ya tafi gidan yayansa da adda. Kasancewar yayan nasa ya makance, bai san yana rike da adda ba.

Yayinda marigayin ke fada masa ya fita masa daga gida, kawai sai Habibu ya daba masa sara sai da ya daina numfashi.

An damke mutane 15 da suka kashe babban jami'in dan sanda

A wani labarin, Yan sanda a jihar Legas sun ce sun kama mutane 12 da ake zargi da hannu wurin kashe babban sufritandan yan sanda Kazeem Abonde a unguwar Ajao da ke jihar.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An tsinci gawar wani mutumi mai aure, da wata Amarya a cikin mota a Kano

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa kakakin yan sandan jihar Legas Adekunle Ajisebutu ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

An kashe tsohon DPOn na Ajangbandi, Mr Abode, ne a ranar 22 ga watan Satumba yayin sumame da suka kai wasu wurare da aka hana amfani da babura a Ajao Estate.

A cewar yan sandan, bata gari masu dimbin yawa ne suka yi kwantar bauna a kofar fita daga unguwan suka kuma far wa yan sandan da bindigu, adduna da wasu muggan makamai hakan ya yi sanadin mutuwar babban dan sandan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng