Yadda na ji da labarin kashe Sheikh Ja’afar ya zo mani ina Saudi inji Zainab Ja’afar Adam
- Malama Zainab Ja’afar Adam ta bayyana irin alakar ta da mahaifinta, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam
- Har yanzu idan Zainab Ja’afar Adam ta tuna da mahaifin na su, ta na iya shiga daki, ta rusa kuka
- Marigayi Ja’afar Adam ya shaku da babban ‘diyarsa sosai, tace sun hadu karshe ne a garin Madina
Kano - Malama Zainab Ja’afar Mahmud Adam tayi hira da BBC Hausa a shirin ‘ku san malamanku’, inda ta bada takaitaccen tarihin rayuwarta.
Legit.ng Hausa ta bibiyi wannan hirar, inda malamar tayi bayanin abubuwa da dama, daga ciki har da bakin cikin da ta yi a lokacin da aka kashe mahaifinta.
Baya ga mahaifinta, daga cikin malamanta akwai Dr. Sani Umar Rijiyar-Lemu. Malamar tayi karatu a Najeriya da kuma cibiyoyi da wata jami’a a Saudi.
A jami’ar Dayyiba da ke birnin Madinah ne wannan malama ta yi karatun Difloma a shekarar 2010. Yanzu tana daf da gama digiri a jami’ar Bayero - Kano.
“Na taso da mahaifin da babban abin da zai ba ka shiri da shi, shi ne dagewa a kan abin da ya shafi karatu. Kuma Allah ya hada ni da miji mai karfafa ta ne a wannan fanni.” - Zainab Ja’afar Mahmud Adam
Alaka ta tsakanina da malam
Shugabar kungiyar mata ta kungiyar Izala ta reshen jihar Kano ta shaidawa BBC, ta yi rashin mahaifinta.
“Ba son kai ba, duk wanda yake da kusanci da Malam ya san irin alaka ta da Malam, da yadda na ke a wurinsa, da yadda yake nuna kauna da tarbiya da kula ta musamman.”
“Ban sani ba ko don ni kadai ce mace a lokacin, duk ‘yanuwa na maza ne a baya, kafin a samu ‘ya mace.
Malam ba mahaifi ba ne kurum a wuri na, kuma rashin shi ya bar gibi, akwai abubuwan da babu wanda zai iya yi mani idan ba shi ba saboda kusancin da ke tsakaninmu.” - Zainab Ja’afar Mahmud Adam
Har yau ina yin kuka
“Gaskiya abu ne da babu dadi, kuma ba na fatan Allah ya saka jarabta ta da irin wannan tashin hankalin, domin mutuwa ce da ta zo kwatsam, babu zato, babu tsammani.”
“Abu ne wanda an shiga damuwa, gas hi a lokacin ina nesa, ban a gida. Duk da ‘yanuwa a Madina sun yi kokarin debe mani damuwar da nake ciki saboda rashin na mu ne duk.”
“Amma dole zuciyata tana fada mani ni kadai na ke jin wannan damuwa. Kuma Allah ya jarabce ni da ban samu zuwa a lokacin da aka yi abin ba.
Sai bayan watanni uku zuwa hudu sannan na dawo, na hadu da ‘yanuwa. Abu ne babu dadi wanda ban cika son yawaita magana a kai ba, domin har yau ban fasa shiga daki in yi kuka idan na tuna shi ba, saboda rashi ne da har in komawa Allah, ba zai daina taba ni ba.” – Zainab Ja’afar.
Wannan Baiwar Allah tace haduwar karshensu da malamin shi ne lokacin da ya zo yin Umrah a kasa mai tsarki, sannan sun yi waya saura kwanaki takwas a harbe shi.
Wasikar Malam zuwa ga 'yarsa
Zainab Ja’afar Mahmud Adam ta biyo mahaifinta wajen son karatun addini da neman ilmin musulunci, mahadacciyar Al-kur’ani ce, kuma mai yin wa’azi.
Kwanakin baya kun ji cewa an tono wasikar da Marigayi Jafar Adam ya rubutowa 'Diyar ta sa shekaru 20 da suka wuce, inda ya hore ta da ibada da karatu.
Asali: Legit.ng