Da duminsa: Yan bindiga sun yi awon gaba da DPO na yan sanda
1 - tsawon mintuna
- DPO na yan sandan Furgar ya shiga hannun masu garkuwa da mutane da suka addabi al'ummar Najeriya
- Yan bindigan sun tare shi a hanya a watan Nuwamba yayinda dogarinsa ya gudu daga cikin motar
- Rahotanni sun nuna cewa yan ta'addan sun kira iyalinsa kuma sun bukaci kudin fansa milyan hamsin
Etsako - Babban jami'n da sanda kuma DPO na ofishin Fugar dake jihar Edo, CSP Ibrahim Aliyu Ishaq, yayi arangama da tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane a jihar Edo.
PRNigeria ta ruwaito cewa yan bindigan sun yi awon gaba da shi ne kusa Rafin Ise dake tsohuwar hanyar Auchi-Ekperi-Agenebode ranar Juma'a.
Rahoton ya kara da cewa tuni sun tuntubi iyalansa kan maganar kudin fansansa.
Gabanin komarwa Edo, CSO Ishaq yayi DPO a ofishin yan sandan Dakata a jihar Kano.
A riwayar Solacebase, yan bindiga sun bukaci kudi N50m kafin su sake shi.
Asali: Legit.ng
Tags: