Jerin kasashe 20 da aka akafi tsadar Kalanzir a duniya, Najeriya ce ta 14
Ranar Laraba, Gwamatin tarayya ta bayyana cewa tana shirin fara rabawa matan rishon girki a fadin kananan hukumomin Najeriya 774.
Ministar harkokin mata, Pauline Tallen, ta bayyana hakan yayin taron kaddamar da horo da hukumar makamashin Najeriya (ECN) ta shirya, rahoton Daily Trust.
Tace sun fahimci mata da yawa na mutuwa, saboda haka suna son tabbatar da cewa kowace karamar hukuma ta samu rishon girki 1000.
Domin amfani da risho wajen girki, sai mutum ya sayi Kalanzir.
Shiyasa Legit.ng Hausa ta ta tattaro wasu Jerin kasashe 20 aka akafi tsadar kalanzir a duniya kawo Nuwamban 2021 bisa binciken Shafin Global Petrol Prices.
Ga Jerin kasashe 20 aka akafi tsadar Litan Kalanzir a duniya :
1. Seychelles - N663.97 ($1.613)
2. Wallis and Futuna - N663.97 ($1.613)
3. Taiwan - N591.93 ($1.438)
4. Belize - N470 ($1.142)
5. Philippines - N462.27 ($1.123)
6. Central African Rep - N456.50 ($1.109)
7. Chile - N453.21 ($1.101)
8. Belgium - N447.86 ($1.088)
9. Mayotte - N433.86 ($1.054)
10. Cyprus - N433.86 ($1.054)
11. Jamaica - N433.86 ($1.054)
12. Aruba - N428.5 ($1.041)
13. Liberia - N428.5 ($1.041)
14. Nigeria - N420.69 ($1.022)
15. Uruguay - N420.69 ($1.022)
16. Malawi - N420.69 ($1.022)
17. Nicaragua - N413.28 ($1.004)
18. Burundi - N412.87 ($1.003)
19. Nepal - N411.22 ($0.999)
20. Cape Verde - N408.75 ($0.993)
Asali: Legit.ng